Alaƙar kayan ƙarin ni’ima da ciwon sanyi

Daga AISHA ASAS

A ‘yan kwanakin baya mun yi darasi mai tsayi da ya shafi ciwon sanyi, abinda ke kawo shi, ma’anar sa, alamomi da sauransu. Kuma a taƙaice mun faɗa cewa, tushe-tushe, ko saka wasu abubuwa a farji da sunan gyara na iya zama silar gayyatar ciwon sanyi.

A wannan satin za mu buɗe wannan darasi da amsa tambayar alaƙar da ke tsakanin kayan mata, ko ince hakin maye ko magungunan ƙarin ni’ima da ciwon sanyi.

Idan mun soma da ainahin kayan da ake haɗawa da sunan ƙarawa mace ni’ima, za mu tarar ababe ne da suka haɗa ababe masu yawa, tun daga tsiro zuwa sauran ababen da Allah ya albarkace mu da su.

Mu ƙadarta cewa, muna amfani da ingantattu daga cikin kayan matan, wanda idan mun yi zancen waɗanda ba su da inganci ko ba su da tsafta, ba sai na yi dogon bayani ba, mun san cewa hatsari ne ga lafiyarmu ma bakiɗaya.

Anan Ina zancen ingantattu kuma tsaftatattu, domin na san wasu za su ce menene illar tunda dai an tsaftace kuma kaya ne da aka tabbatar an yi amfani da ababen da ba sa cutar da jikin ɗan adam.
Bari mu yi amfani da karin maganar nan da ke cewa, “abincin wani, gubar wani,” ma’ana abinda wani ba ya so, kai shi ka ke so, abinda wani zai iya ci ya masa illa, kai za ka iya cin sa ku wanye lafiya, kuma ba don wanda ya ci daban yake da wanda ka ci ba. To shi ma farji hakan yake.

Ba lallai ba ne abinda baki ya ci, ya kwashe lafiya ba, a tusa shi a farji ya yi maraba da shi ba. Wannan na ɗaya daga cikin ababen da ke haddasa mana matsala, amma ba mu cika gane hakan ba.

Bari in bada misali da sinadarin alif. Ko wa ya san aikin alif tsaftacewa, ko zan iya cewa gyarawa ba ɓatawa ba. Da wannan ne wasu suka ga dacewar tsarki da shi don ya wanke ƙwayoyin cuta da ke farji. Sai dai hakan ba haka ba ne, asalima gayyatar cuta ce, kuma hanyar samar da matsala ga wurin ce wadda babu ta a baya.

Farji wuri ne da ke tare da ƙwayoyin cuta, wannan haka ne, sai dai ba kowacce ƙwayar cuta ce daga cikin waɗanda yake tare da su ne yake so ku kawar da su ba, saboda akwai waɗanda yake amfani da su, kuma ayyukan da yake yi suke yuwa tare da su, rashin su kuwa zai kawo tsaiko ga aikin nasu.

Kunga anan ya bambanta da sauran jiki. Shi ya sa aka ce wuri ne da ke buƙatar taka-tsantsan wurin tu’ammali da shi ko yi masa amfani da wasu ababe.

Haka ma idan mun koma ɓangaren kayan ƙarin ni’ima, za a iya samun cikin ababen da aka yi amfani da shi wurin haɗa magungunan akwai wanda zai iya tava zaman lafiyar wurin, hakan kuwa zai iya kawar da wani abu da ba a so ya tafi, ko janyo ciwon sanyi.

A baya mun yi bayani kan yadda sanya turare ko sabulai masu ƙamshi kan iya jefa wurin a hatsarin kamuwa da ciwon sanyi, kuma hakan ba yana nufin darasin namu na wannan makon zai kore wannan batu ba, dukkansu za su iya zama silar samuwar ciwon sanyi da ma wasu curuta na daban.

Bincike na masana ya tabbatar kaso mai yawa daga cikin kayan mata da mata ke tusa wa a farjinsu da sunan qarin ni’ima na canza tsare-tsaren wurin da tun farko aka halicce mace da su, kuma farjin ke walwala da su.

Abinda nake so mata su gane, farjin mace fa bai cin kuɗi wurin kula da shi ba ne, ba kamar fuska ba ne da iya kuɗinki, iya kyan da za ta yi ba, idan za ki riƙe wasu ɗabi’u kawai za ki iya kare wurin, ki samar masa da ƙamshin da ba mai cutarwa ba.

Bari na ba ki misali da ruwan ɗumi, tsare yin tsarki da ruwan ɗumi komai zafi komai sanyi kawai zai iya ba wa mace wani abu da take nema daga wurin. Tsaftace wurin, ta hanyar yawaita canza kamfai, da saurin canja audugar mata a lokacin al’ada, rashin zama a jiƙe, ko zama wuri mai damshi, katange shi daga zuwan ƙwayoyin cuta ta hanyar sa ma sa abinda zai kare shi yayin tafiya ko daga iska da sauransu.