Akwai hanyoyin bunƙasa arziki a sauƙaƙe da ba kowa ya sani ba – Ƙiru

Daga AMINA YUSUF ALI

(Cigaba daga kashi na farko)

Assalamu Alaikum, barkan mu da wannan lokaci. Kamar yadda na yi alƙawari ta hannun Yayata AMINA YUSUF ALI, Wakiliyar Blueprint Manhaja, cewa, idan na samu damar samun wannan shafi na tattalin arziki mai albarka zan bayyana muku wasu hanyoyi da na gano da mutum zai iya zuba kuɗinsa kuma ya samu riba masu kyau in sha Allah.

Kamar yadda na fara kwararo wa masu karatu wasu bayanai na daga dabarun da mutum zai yi amfani da su ya samu bunƙasar arziki a rayuwarsa. 

A makon da ya gabata mun bayyana cewa, mutum ya na samun arziki ne ta hanyar kasafta kuɗinsa ya adana su. Mun fara kawo muku wasu dabarun adana kuɗi, ta manhajoji da dama, yanzu kuma za mu ci gaba. 

2.3. Manhajar Bamboo-Bamboo shi kuma ya ɗaramma Cowrywise, domin kuwa zai ba ka dama ka yi adanin kuɗinka kamar cowrywise sannan ka sayi hannu jari. To amma anan, shi ba ya sayar da hannun jarin Nijeriya sai na ƙasashen waje. Daga cikin kasuwar hannun jarin da yake sayar wa sun haxa da kasuwar hannun jarin Apple Inc, Amazon Inc, The Walt Disney, Microsoft, Netflix, Tesla da sauransu. Wannan jadawalin jerin-gwanon kamfanonin su ake wa laqabi da S&P 500 ETFs. Wato kamfononin da suke da ƙarfin a duniya kuma suke ba da ribar shekara- shekara mai kyau. Sannan idan ba ikon Allah ba, ba a kawo musu tunanin karyewa ko rage daraja. 

Sannan har wa yau a cikin sa akwai Real Estate wato gidaje da kadarori na ƙasar waje (Wasu rukunin gidaje ne, wasu shaguna ne, wasu filayene, wasu gidajen haya ne, da sauransu). Sannan akwai kamfanonin wasanni wato ƙungiyoyi na ƙwallon ƙafa, tseren motoci, Wasan doki (Polo) da sauransu. Duka duka dai idan ka shiga, za ka gansu. za ka lura cewa wasu kuɗin su $14 (N18,000 haka), wasu kuma $100, $350, $500 da sauransu. Dai-dai kuɗinka dai-dai shagalinka. Amma kamar yadda na fada a baya, ka yi bincike akan kamfani kafin ka sayi kasuwar hannun jarin kamfanin. Sannan ka lura sosai kar ka saka kuɗinka a kamfanin da yake sarrafa alade (Pig) ko giya (alcohol) ko caca (Gambling). 

Don ƙarin haske a kan yadda ake amfani da Manhajar Bamboo, za ka iya shiga Youtube ka yi binciken bidiyoyi a kan yadda ake amfani da manhajar Bamboo. Za ka gan su rututu. Shi ma kamar Cowrywise, ya yi hoɓɓasa wajen amfani da dokokin tsaro a ƙarƙashin Hukumar tsaro da chanjin kuɗaɗe, US-Traded Securities, FINRA/SIPC, LLC, Nigerian Exchange Group, Lambeth Capital da sauransu.  

2.4. Risevest
Shi ma Risevest kamar sauran, yana da zaɓi na tsayayyen kuɗin shiga, wato adana kuɗin don ajiya ko don samun ribah (Interest). To amma akwai zaɓin da zai cire maka ribah (Interest) daga tsarin ajiyarka. Shi ma kuma ana iya siyan hannun jari na ƙasashen waje musamman Turai, Indiya, Chana da sauransu. A taƙaice ma, kusan ma zan iya cewa ya fi gabaɗaya biyun da na faɗa a sama idan ana magabar yawan kamfanoni. Sannan yana da zaɓi na harkar filaye da gidaje a Birtaniya, Faransa, Itali, Amurka da sauransu. Sannan duk abinda ka samu zai iya biyan ka a Dala. Kuma za ka iya sayar da hannun jarinka a kowane lokaci. 

za ka iya saya ta hanyar sauke manhajar sannan ka yi rajistar da sunan mai amfani da lambar sirrin da ba za ka manta ba. Daga bisani sai kaje “Create An investment Plan”, sai ka zaɓi kalar kasuwancin da kake so ka yi. Don ƙarin haske akan yadda ake amfani da Manhajar Risevest, za ka iya shiga Youtube ka yi binciken bidiyoyi akan yadda ake amfani da manhajar Risevest. za ka gansu rututu.

Shi ma kamar Cowrywise, ya yi hovvasa wajen amfani da security regulations ƙarƙashin Securities and Exchange Commission, US-Traded Securities, FINRA/SIPC, LLC, Nigerian Exchange Group, Lambeth Capital da sauransu.

2.5. Manhajar Octa Trading:

Shi ma kamar sauran, yana da ɓangarori da yawa tun daga abinda ya shafi sayen kuɗi, sayen hannu jari, sayen crypto, sayen zinare, sayan fetur da sauransu. Bari mu ɗauki kowane ɓangare mu tattauna:

2.5.1. Cinikin canjin kuɗi:

Siffarsa ta farko ita ce Sana’ar Canjin kuɗi, wato kasuwancin kuɗaɗen ƙasashen waje. Babu nau’in din da babu a cikin manyan kuɗaɗe na duniya. za ka iya saka Naira ka sa yi dala, daga nan sai ka yi amfani da dalarka ka sayi wasu kuɗaɗen. 

2.5.2. Kirifto Karansi 

Yana da Ɓangaren cryptocurrency, amma ba na bogin ba, na gasken. Don akwai sulallan Kirifto Karansi na bogi (wanda ake cutar mutane da su) da nagari. Waɗannan manya ne, kuma masu samar da roiba. Amma sai ɗan-karen tsada, magana ake da dubbunnan daloli. Akwai su Bitcoin, EThereum, Cardano, Solana da sauransu. Kuma wani abu da zai ba ka sha’awa shi ne, daga kan Manhajar taka kana kallon yadda kasuwar kadarar ka take tafiya a faɗin duniya. Babu cuta ba cutarwa, kana kallon komai da idonka. 

2.5.3. Kasuwar gwal da azurfa da man Fetur.

Ita ma kasuwar haja ce wadda take ci 24/7 kuma a gabanka kana kallon komai. Sannan akwai kasuwar man fetur da sauran nau’ika na ma’adanai, sai wanda ka zaɓa. 

2.5.4. Manhajar Demo Feature:

Don ka koyi amfani da wannan zauren, kamfanin Octa yana ba ma Demo asusu mai ɗauke da kuɗi a ciki don ka yi amfani da su wajen saye da sayarwa. Hakan zai taimaka maka wajen jarraba kasuwar musayar hannun jari da kuɗin gangan, kafin ka saka kuɗinka na gaske a ciki. 

A kula! Shi ma Octa kamar sauran yana da kyau ka kalli bidiyoyi a kan yadda ake amfani da shi, da kuma yadda kasuwancinsa yake. Kuma har wa yau ina kara jaddada mana cewa kar ka sayi haja sai ka yi bincike a yanar gizo wato intanet kafin ka zuba kuɗinka.

A lura! Shi ma kamar Cowrywise da sauran, ya yi hoɓɓasa wajen amfani da tsarin tabbatar da tsaro ƙarƙashin hukumomin Securities and Exchange Commission, US-Traded Securities, FINRA/SIPC, LLC, Nigerian Exchange Group, Lambeth Capital da sauransu. Kuma yana da maau ɗaukar nauyinsa manya-manya a faɗin duniya wanda suke ba shi kariya da kuma tsaro. 

  1. Naɗewa:

A ƙarshe, idan ba ka gamsu da saka kuɗinka a kamfanoni ta hanyar yanar-gizo ba wato intanet, babu laifi za ka iya tashi ka je kasuwar hannun jari Nijeriya ka samu wakili ya zuba maka hannun jari a kamfanoninmu na gida. Illar kamfanoninmu ita ce, babu garanti da kuma tsaro mai kyau, kuma kasadar ta yi yawa. Za a iya wayar gari wani Manaja ko shugaban zartaswa ya rance kuɗin kamfanin bakixaya, kamar yadda aka yi wa Bank of the North a Nijeriya da irin su Intercontinental Bank da sauransu. 

Sannan yana da kyau ka sani cewa, akwai kasada a kasuwancin kasuwar hannun jari. za ka iya siyan hannun jari a kamfani yau, gobe a ce maka hannun jarin kamfanin ya karye, don haka kai ma ka faɗi. To amma wannan ɗin ba abu ne da yake faruwa ba sosai akai-akai musamman ma idan kai mai tsarin dogon zango ne. 

za ka iya fara jarrabawa da kaɗan da kaɗan har ka yi wayo a cikin harkar. Idan ka gane mata, kuma ka ga za ka iya, sai ka yi expanding. Ni dai ina yi, kuma yanzu haka ina da kasuwar hannun jari na kamfanonin Ashaka, Dangote Cement, Stanbic, UBA, da wasu yan tsirari. 

Zan ƙarƙare wannan rubutu da faɗin Morgan Housel, marubucin littafin “The Psychology of Money”. A inda yake yanko maganar biloniya kuma ɗan kasuwar hannun jari Charlie Munger, cewa mutane da yawa a Amurka in a farkon 1960, da 70, sun samu kuɗinsu ne ta hanyar zuba jari a kasuwar hannun jari. Akwai waɗanda suka fara sayen kasuwar hannun jari da Dala $10. Amma bayan shekara 30, suna da dalar Amurka miliyan ɗari da motsi.

Charlie Munger yake cewa, da ya san haka kasuwar hannun jari suke da ƙarfi, da ya fara siyan hannun jari tun yana da shekaru 13 a duniya. Domin masu kuɗi da yawa na wancan lokacin, sun fara siyan hannun jari tun suna da shekaru 10 zuwa 13. 

A nan zan dasa aya. Allah ya bamu sa a. Allah kuma ya sa mu amfana da wannan rubutu. Wanda suka ƙarfafa ni wajen rubutawa, Allah ya tara mu a ladan. Amin. 

Daga alƙalamin Muhammad Ubale Jadaka Kiru.