An kashe sojoji 15 a Delta – Hedikwatar Tsaro

Daga BASHIR ISAH

Babban Ofishin Tsaro da ke Abuja ya bayyana cewa, jami’ansu 15 sun rasa rayukansu sakamakon rikicin ƙabilanci a Jihar Delta.

A cewar ofishin, jami’an da aka kashe sun haɗa da masu muƙamin Manjo 2, Kyaftin 1, sai kuma ƙananan sojoji 12.

Ya ƙara da cewa, marigayan sun cimma ajali ne yayin da suka je kwantar da tarzoma na rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙauyukan Okuama da Okoloba da ke jihar a ranar Alhamis da ta gabata.

Sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai na rundudunar, Brig. Gen. Tukur Gusau, wadda aka fitar a ranar Asabar ta ce, wasu matsa ne suka kai wa sojojin hari a lokacin da suka je aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin Okuoma da ke Ƙaramar Hukumar Bomadi.

Daraktan ya ce hatta kwamdan da ya jagoranci dakarun zuwa yankin, shi ma ya rasa ransa a harin.

A cewar sanarwar: “Wasu matasa sun yi wa dakarun 181 Amphibious Battalion kwanton-ɓauna a lokacin da suka tafi aikin tabbatar da lumana a yankin Ƙaramar Hukumar Bomadi, Jihar Delta.

“Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis, 14 ga Maris, 2024, biyo bayan kiran da suka samu dangane da rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙauyukan Okuama da Okoloba da ke jihar Delta.”

Gusau ya ce Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Kazalika, ya an sanar da gwamnatin Jihar Deltaabin da ya faru.

Kodayake an samu damƙe wasu da ake zargi da hannu a harin, in ji Gusau.