22
Jun
' Daga HABU ƊAN SARKI a Jos Kwamishinan ýan sanda na Jihar Filato, Emmanuel Olugbemiga Adesina ya tabbatar da kama mutane 22 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya 12 da suka fito daga Zariya a Jihar Kaduna, kan hanyarsu ta zuwa biki a Ƙaramar Hukumar Qua'an-Pan ta Jihar Filato. Ya kuma ƙara da cewa, an kuɓutar da mutane 14 waɗanda babu abin da ya same su, yayin da wasu 21 ke samun kulawar likitoci a babban asibitin Mangu. A wani labarin kuma, ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam ta Jihar Filato ta yi Allah…
