Atiku, Tambuwal da Imoke sun shiga ganawar sirri da Obasanjo

Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya jagoranci wata tawaga don ganawa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a gidansa da ke Hilltop, Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, a ranar Litinin. Atiku ya samu rakiyar tsohon gwamnan Jihar Cross River, Liyel Imoke, da kuma tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Tambuwal.

Har zuwa lokacin da aka kammala taron, ba a bayyana takamammen dalilin ganawar ba, amma ana raɗe-raɗin cewa hakan na da nasaba da shirye-shiryen ‘yan adawa na fitar da dabarun da za su taimaka wajen kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Atiku Abubakar ya kasance mataimakin Obasanjo daga Mayu 1999 zuwa Mayu 2007. A zaɓen 2023, ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar PDP, inda ya zo na biyu bayan Bola Tinubu na APC wanda ya lashe zaɓen. Atiku mai shekaru 78, ya shafe fiye da shekaru talatin yana ƙoƙarin cimma burinsa na zama shugaban ƙasa.

By ukarofi