Soke kwangila: Babu mahajjacin da zai kasa zuwa hajjin 2025 – Shugaban NAHCON

Daga USMAN KAROFI

Shugaban hukumar kula da ayyukan hajji ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh, ya tabbatar da cewa za a gudanar da aikin Hajjin 2025 ba tare da wata matsala ba. Ya yi wannan bayani ne yayin da yake mayar da martani kan wani rahoto da ke cewa “dubban mahajjatan Najeriya na iya rasa Hajjin 2025 saboda soke kwantiragin Masha’ir da shugaban NAHCON ya yi.”

Farfesa Saleh ya ƙaryata wannan labari, yana mai cewa ba gaskiya ba ne, kuma babu wani mahajjaci da zai rasa damar gudanar da ibadar Hajji. Ya bayyana cewa soke kwantiragin da ake magana akai ba daga hukumar NAHCON ya fito ba, illa dai hukumomin Saudiyya ne suka soke kwantiragin kamfanonin biyu da suka dace da Masha’ir. Ya ƙara da cewa ya ziyarci Saudiyya domin fahimtar dalilin soke kwantiragin tare da tabbatar da cewa ba zai shafi shirye-shiryen Najeriya ba.

Shugaban ya bayyana cewa dukkan shirye-shiryen da hukumar NAHCON ta tsara suna nan daram, kuma mahajjatan Najeriya za su yaba da irin matakan da aka ɗauka. Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaba Kashim Shettima bisa amincewar su don gudanar da wannan muhimmin aiki.