’Yan kasuwa na yunƙurin yada fetur ɗin Dangote don rage farashin mai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Masu sayar da man fetur a Njjeriya sun bayyana cewa kuɗin da ake kashewa wajen shigo da man fetur zuwa ƙasar ya ragu zuwa N922.65.

Rahotanni sun nuna cewa sauƙin farashin ya sanya saukar kuɗin litar mai ƙasa da yadda matatar Dangote ke sayarwa a kan N955.

Raguwar farashin ya shafi kuɗin jigilar kaya, harajin shigo da kaya, da kuma tasirin canjin kuɗin waje.

Ana hasashen hakan na nuna yiwuwar masu kasuwancin mai su koma shigo da man fetur daga ƙasashen waje maimakon saye a matatar Dangote.

Wani babban ɗan kasuwa wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa an samu sauƙin farashin shigo da man fetur Nijeriya.

Dan kasuwar ya ce, “Farashin fetur da aka shigo da shi ya fi sauƙi ga masu kasuwanci, don haka ba za ka iya zargin waɗanda suka koma shigo da shi daga ƙetare ba.” 

The Cable ta wallafa cewa raguwar farashin litar fetur da aka shigo da shi zai iya jawo hankalin ‘yan kasuwa su koma kan tsarin shigo da kaya daga waje.

Hakan na zuwa ne bayan an bayyana cewa hauhawar farashin man fetur da aka samu a kwanakin baya ya biyo bayan tsadar ɗanyen mai ne a kasuwannin duniya. 

Duk da wannan raguwar farashi, litar fetur har yanzu tana kan farashi mai tsada a wasu gidajen man Nujeriya, inda manyan dillalai ke sayar da lita tsakanin N990 zuwa N1,010 a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa farashin jigilar kaya da aka ƙiyasta ya dawo N922.65 a ranar Juma’a, wanda ya ragu daga N943.75 da aka sanar a ranar Alhamis. 

Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa wasu gidajen mai sun rage farashin su a wasu jihohin Nijeriya. 

Gidan man NIPCO ya rage farashin daga N965 zuwa N960, yayin da Aiteo ya rage daga N980 zuwa N960. 

A ɗaya ɓagnaren, an ruwaito cewa gidajen man Swift da AA Rano suma sun rage farashin litar mai zuwa N960. A jihohin Delta da Kalaba an cigaba da sayar da litar mai tsakanin N972 zuwa N990.

By ukarofi