Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) sun yi kira ga Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ya zage damtse wajen shawo kan hauhawar farashi, wanda ya ƙaru daga kashi 33.6 a watan Nuwamba zuwa 34.8 a watan Disamba.
A yayin wani taron tattaunawa, babban manazarci a Bankin Duniya, Sameer Matta, ya ce wajibi ne CBN ta ci gaba da mai da hankali wajen daƙile wannan matsala.
Ya kuma jaddada buƙatar inganta samar da kayayyaki, musamman a ɓangaren noma, da bunƙasa haɗin kai tsakanin karkara da birane, tare da sake duba manufofin haraji a wasu ɓangarori.
A nasa ɓangaren, jakadan IMF a Nijeriya, Christian Ebeke, ya yi kira da a samu haɗin kai mai ƙarfi tsakanin manufofin tattalin arziki da na kuɗi don tabbatar da nasarar rage hauhawar farashi. Ya yaba wa ƙoƙarin CBN da hukumomin kuɗi na gwamnati wajen daƙile matsalar lamunin kasafin kuɗi da kuma inganta yanayin tattalin arziki.
Ya yaba da yadda babban bankin ƙasa da kuma hukumomin kuɗi suka himmatu wajen ƙarfafa haɗin kai, wanda ya taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki.
Ebeke ya kuma jaddada muhimmancin magance matsalar raba gardama na sauye-sauye, kamar cire tallafin man fetur da sake fasalin Naira, domin kare al’umma masu rauni. Ya bayyana rawar da manufofin kasafin kuɗi ke takawa wajen daidaita ayyukan kuɗi da kuma buƙatar matakan kare lafiyar jama’a.
Ebeke ya jaddada cewa matakan da aka ɗauka na cire tallafin man fetur da kuma gyare-gyaren darajar Naira suna da muhimmanci, amma dole ne a kare marasa galihu daga illolin da matakan ka iya haifarwa.
Haka zalika, Matta ya ja hankalin gwamnati kan muhimmancin ci gaba da aiwatar da shirin kariyar halin da mutane suke ciki da hanzarta bayar da tallafi ga talakawa.
Ya kuma yi gargaɗi cewa rashin ɗaukar matakai na gyara tattalin arziki zai ci gaba da haifar da asara mai yawa, inda tallafin man fetur da na musayar kuɗaɗe ke laƙume kashi biyar cikin ɗari na GDP na ƙasar. Wannan, inji shi, babban ƙalubale ne ga cigaban tattalin arzikin Nijeriya.
