Gwamnatin Tarayya ta buɗe ƙofar zuba jari a ɓangaren lantarkin Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ɓangaren wutar lantarki a Nijeriya a buɗe don saka hannun jari a taron #Mission300 na Makamashi na Afirka da aka gudanar a Dar es Salaam, Tanzania.

Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga zaɓaɓɓun masu zuba jari da abokan hulɗar ci gaba a yammacin ranar Litinin.

Edun ya bayyana ɓangaren wutar lantarkin Nijeriya a matsayin babbar dama ta zuba jari. Ya jaddada ƙudurin al’ummar ƙasar na samar da daidaiton tattalin arziki, da tsaftataccen burin makamashi, da samun damar samun makamashi a duniya baki ɗaya.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar na ma’aikatar kuɗi a shafin Tuwita a ranar Litinin.

Kimanin kashi 80 cikin 100 na mutanen da ba su da wutar lantarki a duniya suna zaune ne a Nijeriya da sauran ƙasashe a yankin kudu da hamadar Sahara, duk da raguwar sama da miliyan 10 a cikin wannan al’umma, a cewar wani rahoto.

Hukumar kula da makamashi ta duniya IEA, a rahotonta na baya-bayan nan na kasa kan samun wutar lantarki, ta bayyana cewa adadin mutanen da ke fama da rashin wutar lantarki ya ragu daga sama da miliyan 760 zuwa kasa da miliyan 750 a cikin shekarar da ta gabata.

By ukarofi