Harkokin kasuwanci sun dawo a garin Batsari

Spread the love

Daga ABDULLAHI Muhammad a Katsina

A yayin da harkar tsaro ta inganta a garin Batsari, harkokin kasuwanci ya dawo a manyan kasuwannin ƙaramar hukumar Batsari a Jihar Katsina.

Karamar hukumar Batsari na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ‘yan ta’adda suka lalata a jihar.

Ɗaruruwan mutane suka rasa rayukansu,wasu sun raunana wasu kuma sun yi gudun hijira zuwa Katsina da jamhuriyar Nijar sakamakon hare haren yan ta’adda a yankin.

Haka kuma sun ƙone kasuwannin da ɗaruruwan gidaje musamman a ƙauyukan da suke kewaye cikin garin Batsari,ga rufe makarantu.

Sai dai shugaban ƙaramar Batsari Salisu Mamman da yake hira da manema labarai a ofishin sa ya ce yanzu zaman lafiya ya fara dawo a ƙaramar hukumar.

“Al’ummar ƙaramar hukumar na tafiyar da harkokin su na yau da kullum, manyan kasuwannin an buɗe ana ta hada hadar kasuwanci, manoma musamman na karkara sun koma gonakin su”inji Ifo.

Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana nasara da aka samu na dawo da zaman lafiya a yankin da irin ƙoƙari da jajircewa na gwamna Dikko da samar da duk abin da yakamata ga jami’an tsaro a ƙaramar hukumar.

Mataki na farko da malam Dikko ya ɗauka shine ƙirƙirar jami’an tsaron al’umma (CWC) da samar masu da duka kayan aikin da ya dace na yaƙar ‘yan ta’adda a ƙaramar hukumar wanda hakan ya yi tasiri a cewar sa.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara da cewa gwamnan ya kuma samar da motoci masu sulke ƙirar APC a ƙananan hukumomin takwas da ke fama da matsanancin rashin tsaro.

Ya bayyana cewa bayan waɗan nan motocin yaƙi da gwamna ya basu,su a matakin ƙaramar hukuma sun samar wa jami’an tsaron motoci na sintiri guda huɗu.

Shugaban ƙaramar hukumar ya sanar da cewa hukumar raya ƙasa na majalisar ɗinkin duniya (UNDP) na nan na shirin gina gidaje 152 wa yan gudun hijira a yankin.

“Haka kuma gwamnan na taimaka wa waɗannan kananan hukumomi da man fetur ga motoci na jami’an tsaron da ke yaƙar yan ta’adda a yankunan”ya sanar da haka.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce duk da rashin tsaro a yankin, ƙaramar hukumar ta aiwatar da muhimman ayyuka na raya ƙasa.

Ya bayyana gyara wata babbar sakandare na al’umma da tai shekara fiye da 40 ba a karatu saboda rashin gyara ga kuma rashin tsaro a yan shekarun nan.

“Da amincewar gwamna Dikko Raɗɗa ƙaramar hukumar ta kashe Naira Miliyan 82 wajan gyaran makarantar”inji Salisu Mamman.

Sai shugaban ƙaramar hukumar ya yi kira ga sauran waɗanda suka ƙauracewa ƙauyukan su da su dawo su cigaba da hidimar su na yau da kullum.

Ya ce gwamnatin Jihar Katsina da haɗin gwiwa da ƙaramar hukumar sa, ta ɗauki matakai da tabbatar da dauwamamman zaman lafiya a yankin da jiha baki ɗaya.

By ukarofi