Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da ta karɓa daga ‘yan kishin jihar. Fim ɗin na fuskantar zargi kan amfani da kalma da ake ganin tana da ma’ana ta batsa, wanda ya sa hukumar ta dakatar da shi tare da gayyatar dukkannin waɗanda suka fito a ciki domin jin ba’asi.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ne don kare martabar al’adu da ɗabi’un mutanen Kano. Ya ce kwamitin da aka kafa zai binciki batun, kuma duk wanda aka gayyata bai amsa kira ba, zai iya fuskantar hukunci daga hukumar.
Fim ɗin Zarmalulu na fuskantar suka daga wasu ‘yan masana’antar Kannywood da suka bayyana damuwarsu kan irin kalmomin da ake amfani da su a fina-finai, musamman waɗanda ke shafar tarbiyya da al’adar yankin.
Hukumar tace fina-finai ta Kano ta sha bayyana matsayinta na kare kyawawan dabi’u a masana’antar, kuma tana cigaba da sanya idanu kan fina-finai domin tabbatar da cewa an bi dokoki da ƙa’idojin tacewa da aka gindaya a jihar.
