Gwamna AA Sule ya koka da sayar da guraben aiki ga malamai 2,277 a Nasarawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana yadda jami’an gwamnati suka sayar da guraben aiki ga masu neman aikin koyarwa guda 2,277 a jihar.

Ya kuma yi barazanar miƙa al’amarin ga jami’an Hukumar Kula da Malamai ta jihar (NSTSC) da aka dakatar daga aiki ga hukumomin tsaro, bisa zargin su da karɓar kuɗaɗe daga hannun waɗanda ke neman aikin karantarwa.

Lamarin ya biyo bayan karɓar rahoton kwamitin bincike game da badaƙalar da aka yi na ɗaukar malamai a NSTSC ne da AA Sule ya yi a Fadar Gwamnatin jihar.

Ya bayyana hakan a matsayin abinda ya saɓa wa tsarin gwamnatinsa, ya na mai cewa lallai sai hukumomin tsaro sun shigo ciki tare da tabbatar an mayar wa kowa kuɗinsa.

Ya ƙara da cewa, jami’an NSTSC’n da aka dakatar ba su yi wa kansu da jihar adalci ba, saboda a madadin ɗaukar malamai 1,000 aiki, sai suka ɗauki 3,277.

“Ta ya za mu iya ɗaukar malamai 3,277 a Jihar Nasarawa yau? Ina za ka samu kuɗin da za ka biya su? Ina za ka tura su?”

Gwamnan ya kuma nuna damuwa kan ƙwarewar waɗanda aka ɗauka aikin, a inda ya ce lallai sai an sake tantance su ta yadda za a tabbatar da waɗanda suka cancanta daga cikin gurabe dubun da aka ware.

Har’ilayau, AA Sule ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta biya waɗanda suka ƙaru akan guda dubu ɗayan albashi, waɗanda daga bisani kuma sai a sallame su.

By Babaji