
Rahoton Kimanta Ayyukan Jihohi na Phillips Consulting (pSPI) na shekarar 2025 ya sanya Jihar Kaduna a matsayi na uku cikin jerin jihohin da suka fi nuna kyawawan ayyuka a Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na Jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki, ya fitar, gwamnatin jihar ta ce wannan matsayi wata shaida ce da ke tabbatar da nasarar manufofi da gyare-gyaren da gwamnatin Uba Sani ke aiwatarwa domin inganta rayuwar al’umma.
Sanarwar ta bayyana cewa rahoton ya yi la’akari da muhimman fannoni da suka hada da shugabanci nagari, kula da kudaden gwamnati, bunkasa tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, noma, tsaro da kuma shigar da kowa cikin harkokin ci gaba.
Maiyaki, ya ce muhimmancin wannan yabo shi ne kasancewarsa daga wata cibiyar bincike mai zaman kanta da ta hada bayanan aiki na zahiri da kuma ra’ayoyin jama’a wajen tantance ayyukan gwamnatoci.
“Wannan matsayi ya nuna cewa Kaduna na ci gaba da samun ci gaba wajen karfafa cibiyoyin gwamnati, inganta shugabanci da kuma samar da karin damammaki ga al’ummar jihar,” in ji shi.
Kwamishinan ya Kara da cewa wannan ba shi ne karon farko da Kaduna ke samun irin wannan yabo ba. A farkon shekarar nan, jihar ta zama ta farko a Nijeriya a rahoton kungiyar ( Transparency and Integrity Index (TII) 2025) ta wallafa, inda kuma ta samu mafi girman maki a fannin yaki da cin hanci da rashawa.
Maiyaki, ya bayyana cewa wadannan nasarori suna nuna irin tasirin sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa tare da zuba jari a muhimman bangarori domin bunkasa rayuwar jama’a.
Ya jaddada cewa duk da samun irin wadannan lambobin yabo, gwamnatin jihar za ta ci gaba da mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’umma ta hanyar ci gaba mai anfani ga kowa, karfafa tattalin arziki, samar da ingantattun ayyukan gwamnati da kuma tabbatar da dorewar zaman lafiya.
Maiyaki ya sake tabbatar da kudurin gwamnatin Uba Sani na gina Kaduna mai zaman lafiya, wadata, gaskiya da kuma jihar da za ta iya gogayya da sauran jihohi a matakin kasa da kasa.
A kan hakan, gwamnatin jihar ta yabawa al’ummar Kaduna, abokan hulda na ci gaba, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, kungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.
