
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar da ke jagorantar teburin Frimiyar ƙasar Ingila, wato Liverpool, ta yi rashin nasara da ci ɗaya da nema a hannun Plymouth a wasan kofin FA, wanda hakan ya nuna an yi waje da ita a gasar na wannan kakar.
Hakan ya rushe tsammaninta na lashe kofuna huɗu da ta ke ciki inda a makon da ya gabata ne ta kai wasan ƙarshe a gasar Carabo.

Yanzu haka dai Liverpool ita ce ta ɗaya a Frimiya lig da ratar maki shida da kuma kwanten wasa ɗaya.
A minti na 53 ne ɗan wasan Plymouth, Ryan Hardie ya zura ƙwallo a ragar Liverpool a bugun daga kai sai mai tsaron gida, wato fenareti, wanda haka ya ba su damar kai wa zango na biyar a ‘FA Cup’.
