Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Nijeriya da Saudi Arabiyya sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimta domin ƙarfafa yaƙi da hada-hadar ƙwayoyi.
A ranar Litinin Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA ta Nijeriya da kuma Hukumar da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Saudiyya GDNC, suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Riyadh.
Cikin wata sanarwar da daraktan yaɗa labarai na hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ya ce ƙasashen biyu sun amince su ƙara ƙarfafa yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a dukkan iyakokinsu.
Da ya ke magana a wajen sanya hannu kan yarjejeniyar, shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa, mai ritaya, ya ce dukkan ƙasashen sun jima suna yin haɗaka da ɓangarori daban-daban.
Marwa, wanda ya samu rakiyar darakta a sashen bincike da gudanarwa na hukumar, Ahmed Ningi, ya ce dukkan ƙasashen na da kyakkyawar alaƙa a tarihi.
Ya ce,” A yau rana ce ta musamman mai matuƙar muhimmanci ga dukkan ƙasashen biyu.
“Yau rana ce da ta ƙara kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu, musamman hukumomin da ke yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi,” inji Marwa.
Da ya ke bayani a game da muhimmancin yarjejeniyar, Marwa, ya ce hada-hadar da miyagun kwayoyi ta zamo babban kalubale a duniya wanda ke buƙatar ɗaukar ƙwakkwaran mataki.
Ya ce a duk inda ake ta’ammali da ƙwayoyin masu illa to akwai babbar barazana ga al’ummar da ke wajen.
