Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen ƙasar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

A Jamhuriyar Nijar gwamnatin ƙasar ta bayyana Hausa a matsayin harshen da za a rinƙa amfani da shi a ƙasar yayin da sauran harsuna ta ayyanasu a matsayin na magana.

Kazalika an kuma bayyana harshen Ingilishi da Faransanci a matsayin harsunan aiki.

To sai dai kuma ba dukkanin ‘yan kasar ne ke maraba da wannan mataki ba.

An ƙiyasta cewa akwai mutum miliyan 18 da ke jin harshen hausa a Jamhuriyar Nijar, abin da ake ganin wannan ne ya sanya gwamnatin kasar ta ayyana shi a matsayin harshen da za a rinka amfani da shi a ƙasar.

To sai dai kuma ba dukkanin ‘yan ƙasar ne wannan mataki ya yi wa daɗi ba, inda wasu ke cewa ya kamata a yi nazari sosai a kai.

Harshen Hausa shi ne ke matsayin na uku a Afirka inda ƙasashe da dama a Afirka a ke samun masu jin harshen.

Akwai dai masu jin harshen Hausa a ƙasashe kamar Nijeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da Chadi da Sudan da Benin da Togo da Gabon da kuma Burkina Faso.

By ukarofi