Farashin kayayyaki a Nijeriya ya hauhawa a watan Maris – NBS

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Farashin kayayyaki ya hauhawa a watan Maris da ya gabata zuwa kashi 24.23 cikin 100 a sababbin alƙaluman da aka koma amfani da su a Nijeriya.

Rahoton da hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta fitar a ranar Talata ya nuna cewa an samu ƙarin hauhawar farashin da kashi 1.05 idan aka kwatanta da watan Fabrairu na 2024 daga 23.18 da aka samu a watan.

Wannan ne karon farko da aka samu ƙarin hauhawar farashin a Nijeriya tun bayan da hukumar National Bureau of Statistics (NBS) ta sauya ma’aunin da take amfani da shi wajen fitar da alƙaluman a farkon shekarar nan.

“Bugu da ƙari, alƙaluman saurin hauhawaar farashin ya kai 3.90% a watan Maris na 2025 idan aka kwatanta da na Fabrairu, wanda yake 2.04%,” a cewar rahoton.

Ta ƙara da cewa bisa lissafin shekara-shekara, hauhawar kayan abinci kuma ta kai kashi 21.79 a watan Maris ɗin na 2025 idan aka kwatanta da Maris na 2024.

Ta ce abubuwan da suka fi jawo hauhawar farashin sun haɗa da abinci da kuma lemukan sha na kwalba (kashi 9.28 cikin 100), da kuɗaɗen hayar gida da na wuraren sayar da abinci (kashi 2.99 cikin 100), da kuɗin sufuri ((kashi 2.47 cikin 100).

Sauran su ne kuɗin ruwa, wuta, iskar gas da sauran makamashi, ilimi, sai kuma harkokin lafiya.

By ukarofi