Ɗan POS ya kashe kansa bayan an damfare shi miliyan N2.5

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani bala’i ya afku a ƙaramar Hukumar Ini da ke Jihar Akwa Ibom, yayin da wani matashi mai sana’ar POS mai suna Utibe Eteffia ya kashe kansa bayan da wasu ’yan Yahoo suka damfare shi zunzurutun kuɗi Naira miliyan biyu da rabi.

Eteffia, wanda aka ce yana da shekaru 30 a duniya, ana zargin ya sha wani abu mai guba bayan da masu aikata laifukan yanar gizo — waɗanda aka fi sani da ’Yan Yahoo — suka damfare shi kuɗin. Lamarin dai ya faru ne jim kaɗan bayan da ya yi tsokaci kan tunanin kashe kansa ta shafukan sada zumunta.

A ɗaya daga cikin rubutunsa na ƙarshe, Mista Utibe ya yaɗa hoton kyandir da aka kunna tare da taken, “Shin kun yarda da rayuwa ta biyu?” Ya kuma buƙaci abokansa zama masu son ’yan uwansu ta wajen nuna ƙauna da kuma taimaka wa mabuƙata.

Makwabtansa, waɗanda ke cikin alhini, sun tabbatar da cewa saurayin ya kasance ba ya magana sosai tsawon kwanaki kafin mutuwarsa, yawanci yana zama a gida kuma yana yin dogon kira ta waya har cikin dare.

Yana rayuwa ne a kan titin Akpakoruk da ke Atan Ofot, a unguwar Uyo, kuma yana yin sana’ar PoS ne a bakin titi ɗaura da sakatariyar aungiyar ‘yan jarida ta ƙasa (NUJ), kafin rasuwarsa,” wani makwabcin da aka fi sani da Eka Baby ya bayyana.

Aniefiok Isang, wanda ya bayyana kansa a matsayin abokin cinikinsa kuma makwabcinsa, ya ce: “Wani lokaci, ya kan zauna a gidansa yana kuka, a wasu dare ya kan yi kira ga mutane har zuwa ƙarfe 4:00 na asuba”

“Kusan mako guda kafin kashe kansa, sai ya zo gidana, ya tambaye ni ko ina da gubar ɓera, da na fara tambayarsa, ya bayyana min cewa yana so ya yi amfani da ita wajen mganin wasu ɓeraye a gidansa ne.

“An kuma ce min ya je wani shagon sayar da magunguna da ke unguwar domin duba sinadarin kuma ya yi nasarar sayo guda kafin ya tafi ƙauyensu domin kawo ƙarshen rayuwarsa,” inji Ubong Idem, wani mazaunin Atan Ofot.

Marigayin wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Ini, ya rasa mahaifansa biyu tun yana ƙarami, an ce ƙanwar mahaifinsa ce ta raine shi, wadda ta ga ya yi makarantar sakandare, kuma ya samu tallafin kuɗi daga ‘yan uwa da abokan arziki don gudanar da sana’ar PoS.

ƙoƙarin gano tsayawa da ƙafafunsa, an ce ya shiga ƙulla yarjejeniya ta yanar gizo da masu aikata laifuka, inda suka shigar da shi cikin ƙungiyar asiri da ke gudanar da kasuwanci na Yahoo-Plus, kuma aka yi ta yaudararsa.

An tattaro cewa shigarsa a cikin ƙungiyar asirin ya rikitar da tunaninsa, wanda hakan ya sa zai iya yin duk abin da suka ce masa ya yi.

A cewar wata majiya mai tushe, a lokacin da ya isa gida bayan ya yi tafiya mai nisan kusan mintuna 45 daga Uyo zuwa ƙaramar hukumar Ini, an ce ya tambayi ƙanin mahaifinsa da wasu ko za su je coci, sai suka amsa da cewa ba abin da ke ake yi a cocin a ranar, suka ce sun gwammace su yi addu’a a gida.

A lokacin ne aka ce ya nemi kawun ya bashi kuɗi, amma kawun ya bayyana masa cewa yana da Naira 10,000 ne kacal, inda ya yi ta gunaguni da cewa, “Me Naira 10,000 za ta iya yi?

Da yamma, an ce ya tafi coci kuma ya dawo bayan sa’o’i, inda daga bisani kuma ya haɗiyi gubar.

An gano gawarsa babu rai a barandar, abin da ya ba iyalansa mamaki, inda suka aike da tawaga domin su binciki gidansa domin neman wata shaida da ke da alaƙa da mutuwarsa.

“Ba za mu binne shi yanzu ba har sai mun san dalilin da ya sa ya yanke shawarar kawo ƙarshen rayuwarsa,” inji wata majiya ta dangin sa.

By ukarofi