Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Afirka ta Kudu ta miƙa goron gayyata ga Nijeriya don karɓar baƙuncin taron G20 a Abuja, tayin da ka iya nuna kusantar haɗin gwiwa tsakanin manyan ƙasashen biyu na tattalin arzikin nahiyar.
An tattaro cewa Ronald Lamola, Ministan Harkokin Wajen Afrika ta Kudu ne ya yi wa takwaransa na Nijeriya goron gayyata, a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da taron shugabannin G20 na shekara-shekara, wanda ya haɗa da kasashe 19 tare da Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka, wanda zai gudana a watan Nuwamba a Johannesburg.
Yayin da har yanzu ba a tabbatar da taron da Nijeriya za ta karɓi baƙunci ba, zai zama alama ce ta hannun Nijeriya kai tsaye a G20, ya zuwa yanzu.
Yayin da ƙasar ba ta taɓa zama mamba na dindindin ba, ta taɓa halartar taron a ƙarƙashin shugabannin da suka gabata, na baya-bayan nan a Indiya a 2023, da kuma a baya a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta hanyar shirye-shirye kamar G20.
A wannan shekara, Afirka ta Kudu, wacce ke riƙe da shugabancin G20 tun daga Disamba 2024, tana mai da hankali kan abubuwan more rayuwa na dijital (DPI), bayanan sirri, da haɗin gwiwar duniya a cikin sauye-sauyen yanayi da tattalin arziki.
Sai dai tuni zaman dar-dar ke ƙara ta’azzara gabanin taron, inda shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar ƙauracewa taron baki ɗaya, saboda ikirarin gallaza fararen fata, da suka haɗa da kwace filaye da kisan kiyashi a Afirka ta Kudu.
“Suna ƙwace gonakin farar fata, sannan kuma suna kashe su da iyalansu. Kafofin yaɗa labarai sun ƙi bayar da rahoto kan hakan,” Trump ya wallafa a shafinsa na True Social. “Amurka ta dakatar da duk wani gudunmuwa ga Afirka ta Kudu. Shin ta ya za mu shiga G20? Ba na ganin hakan zai yiwu!”
A farkon shekarar ne Trump ya dakatar da duk wani nau’i na taimakon kuɗi ga Afirka ta Kudu bisa zargin kwace filaye daga hannun manoma farar fata da kuma cin zarafin da ake yi musu.
A yayin da yake mayar da martani game da furucin, mai magana da yawun shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce ba sa sa ran Trump zai halarci taron.
Jam’iyya mai mulki ta yi watsi da ikirarin Trump a matsayin “labarin ƙafe”, inda ta zarge shi da yin amfani da taƙaddama don gujewa fuskantar takwarorinsa na duniya bayan sanar da ƙarin harajin da masu suka suka yi wa laƙabi da ‘zagon ƙasa ga tattalin arziki”.
Amurka ta kuma kori Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu, a watan Maris, saboda “cin zarafi.”
