Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mazauna garin Emure Ekiti na jihar Ekiti sun ɓarke da murna yayin da Shugaban Hukumar Kare Muhalli ta jihar, Bayo Ajayi, ya buɗe wata cibiyar cajin waya domin magance matsalar rashin caji da al’umma ke fuskanta saboda ƙarancin wutar lantarki.
A cikin wani faifan bidiyo da ke zagaye a shafukan sada zumunta, Ajasi ya ce ginin, wanda ya zo a matsayin agaji na wucin gadi a cikin ƙalubalen wutar lantarki na jihar, za a riƙa caja wa al’umma wayoyin su kyauta.
Ina farin cikin kasancewa tare da ku a yau a BAO Agenda Emure. Abin da muke ƙaddamarwa shi ne cibiyar caji, wanda aka yi shi bisa babban dalili: Emure ta daɗe ba tare da wutar lantarki ba, kuma mun gano cewa mutane da yawa suna kokawa don cajin na’urorin hannu. Yayin da gwamnatin jihar ke ƙoƙarin dawo da wutar lantarki, muna samar da wannan wurin a matsayin mafita na wucin gadi har sai an warware matsalar.
Ya jaddada cewa mazauna yankin ba za su biya ko sisin kwabo don yin amfani da wannan wuri ba, inda ya bayyana cewa shirin na da nufin tallafa wa ƙoƙarin gwamnati da kuma tsayawa tare da jama’a.
A yayin ƙaddamarwar, wasu daga cikin al’ummar yankin sun nuna jin daɗinsu ta hanyar waƙoƙin yabo ga jami’in gwamnati. An dai ji taron jama’a na rera waƙoƙin yabo, inda da yawa daga cikin mazauna garin suka fito fili suka yi masa godiya bisa wannan matakin da ya ɗauka a kan lokaci.
An buɗe cibiyar cajin ne tare da wasannin gida kamar Ayo Olopon (wasan allo na gargajiya na Nijeriya, wanda ya shahara a tsakanin ƙabilar Yarbawa), da sauran su.
A halin yanzu, ci gaban ya haifar da ra’ayoyi daban-daban daga Netizens, tare da wasu suna yaba shi a matsayin agaji a kan lokaci yayin da wasu ke tambayar tasirinsa na dogon lokaci.
