28
Nov
Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa Najeriya ta samu kuɗaɗen zuba jari daga waje har Dalar Amurka biliyan 1.27 daga ƙasashen BRICS zuwa watan Juni 2024. Wannan ya nuna ƙaruwar kuɗaɗen da aka samu idan aka kwatanta da Dalar Amurka miliyan 438.72 da aka samu a irin wannan lokaci a shekarar 2023. Ƙasashen BRICS sun haɗa da Brazil, Rasha, Indiya, Sin, da Afirka ta Kudu, tare da sabbin mambobi kamar Iran, Masar, Habasha, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. A lokacin taron China-Africa Inter-Bank Association Forum da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, Shettima wanda ya samu wakilcin mai…
