Kamfanoni sun kama hanyar rage farashin siminti da kaso mai ma’ana

Daga BASHIR ISAH

Kamfanonin siminti a Nijeriya sun amince su saukar da farashin buhun suminti mai nauyin 50kg zuwa tsakanin N7,000 da N8,000.

Kamnonin sun ce za su saukar da farashin ba da ɓata lokaci ba da zarar Gwamnatin Tarayya cika shariɗin da aka cimma a yarjejeniyar da aka yi.

An cimma wannan yarjejeniya tsakanin kamfanonin da lamarin ya shafa da kuma ɓangaren gwamnati ne a wajen taron da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi ya shirya ranar Litinin a Abuja.

Uzoka-Anite ya ce gwamnati ta ba da himma wajen ganin ta daƙile dalilan da suka haifar da tashin farashin siminti da sauran kayayyakin masarufi a faɗin ƙasa.

Mahalarta taron sun haɗa da Ministan Cinikayya Masana’antu da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anite da sauransu.

A baya-bayan nan, farashin siminti ya tashin da ba a taɓa ganin irinsa ba inda ake sayar da buhu kan N10,000 a wasu sassan Nijeriya.