Daga AMINA YUSUF ALI
A halin yanzu dai Bankin ba da lamunin Duniya (IMF) ya shawarci ƙasar Nijeriya da ta qara cire tallafin fetur da tallafin kuɗin lantarki.
Bankin ba da Lamuni na Duniya (IMF), ya bayyana cewa, ya ba da wannan shawara ga Nijeriya na ƙara cire ɗan sauran tallafin fetur da tallafin kuɗin wutar lantarki, domin ta magance matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin ƙasar.
IMF ta ce barin kuɗaɗen tallafin su ne ke ƙara damalmala tattalin arzikin Nijeriya.
Bankin ya ce kuma wannan matsala ta tallafi ce ke ƙara rura wutar talauci da matsalar abinci.
A cikin rahoton da IMF ya fitar kan Najeriya, IMF ya bayyana muhimmancin cire tallafin fetur da na wutar lantarki domin a karkatar da maƙudan kuɗaɗen tallafin da gwamnati ke ɗaukar nauyin biya wajen yin ayyukan raya ƙasa da raya al’umma da kuɗaɗen.
IMF ya bayar da wannan shawara ce a halin yanzu da ake tsakiyar fama da raɗaɗin tsadar rayuwa da masifar tsadar kayan abinci, wadda ba a taɓa fuskantar irin ta ba a tarihin Nijeriya.
Amma kuma IMF ya ba da shawarar cewa gwamnati ta ɗan yi wa marasa galihu wani ɗan ihisanin rage masu raɗaɗin tsadar rayuwa.
“Tallafin fetur da tallafin kuɗaɗen wutar lantarki waɗanda gwamnati ke biya, talakawan da ake yi don su ba su samun alfanun abin. Don haka, a cire tallafin kwata-kwata. Amma gwamnati ta yi wa marasa galihu ɗan ihisanin rage masu raɗaɗin tsadar rayuwa, bisa la’akari da halin tsadar kayan masarufin da ake fama da shi.” Inji IMF.
Idan ba a manta ba, Nijeriya ta cire tallafin man fetur a ranar 29 ga Mayu, 2023 da nufin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuɗaɗen. Lamarin dai ya haddasa mummunar tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci wanda ba a tava fuskanta ba a ƙasar.
Wannan masifa ta kai ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bayyana wasu shirye-shiryen rage raɗaɗin tsadar rayuwa, amma har yanzu shiru talaka bai ga komai a ƙasa ba.
Yayin da gwamnatin tarayya ke ƙara samun kuɗaɗen shiga a kullum fiye da gwamnatin da ta gabata, an rasa abin da ake yi da kuɗaɗen ganin yadda a kullum kuma gwamnatin da ‘yan Nijeriya sai ƙara nausawa cikin masifar durƙushewar tattalin arzikin ƙasa da tsadar rayuwa ake yi.
