Ƙuncin rayuwa: NLC ta nemi a ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa Naira miliyan 1

Daga AMINA YUSUF ALI

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya, NLC ta bayyana cewar idan har tsadar rayuwar da ƙasar ke fama da shi ta ci gaba ko shakka babu ba su da zavin da ya wuce su miƙa buƙatar neman Naira miliyan guda a matsayin mafi ƙarancin albashi.

A wata zantawarsa da manema labarai Mista Joe Ajaero, shugaban ƙunyiyar NLC ta yanzu, ya koka da yadda rayuwa ke ci gaba da yi wa ‘yan Nijeriya tsada tun bayan hawa mulkin shugaba Bola Tinubu sakamakon cire tallafin man fetur da wasu manufofin kuɗi da ya ce dole su ƙalubalance su.

Kafin yanzu dai, NLC na neman Naira dubu 200 ne a matsayin mafi ƙarancin albashi kuma har zuwa wannan lokaci gwamnatin Nijeriyar ba ta sahale buƙatar tasu ba, sai dai Mista Joe Ajaero ya ce a wancan lokaci ana canza duk dalar Amurka guda ne a kan Naira 800 zuwa 900 sabanin yanzu da farashin ke tasamma dubu 1 da 500.

Har zuwa yanzu dai ana biyan ma’aikatan Nijeriya ne naira dubu 30 a matsayin mafi ƙarancin albashi, kuma duk da haka wasu jihohin ba su iya cika wannan mataki.

Wasu rahotanni na cewa har zuwa yanzu akwai jihohin da ke biyan karancin albashi a ƙasa da dubu 10.

Tsadar rayuwa na ci gaba da tsananta a sassan Nijeriya bayan da farashin kayakin abinci ya yi tashin gwauron zabi inda ake sayar da buhun shinkafa a farashin Naira dubu 60 zuwa 70.

A ɓangare guda ana sayar da duk buhun masara guda a farashin naira dubu 56.