Kiɗa a Ƙasar Hausa

Daga HAFIZ ADAMU KOZA

Gabatarwa:

Ana zaton ɗan Adam ya fara amfani da kiɗa ne a lokacin da ya fara neman abinci ta hanyar farauta. Daga nan kuma da mutane suka fara yaƙe-yaƙe a tsakaninsu, sai sana’ar kiɗa ta ƙasaita (Ibrahim, 1983:vii). Masana adabi da al’adun Hausawa suna ganin busa ita ce abu na farko da Hausawa suka fara fahimta a matsayin wani nau’i na kiɗa (Salihu, 1985:1).

Hausawa mutanen farko, sun fara amfani da wannan amo don yin sadarwa da kuma faɗakarwa. Sukan yi amfani da ƙaho wajen faɗakar da junansu bisa wani abu na murna ko na tsoro ko sanar da ganin wani naman daji da makamantan haka. Bayan Bahaushe ya sami ƙaho, sai kuma ya fahimci dabarar samar da amo ta amfani da dutse a matsayin gangar dutse.

Akan yi wannan ganga ne inda za a sami dutse matsakaici a dinga kaɗawa da wani dutsen ƙarami tamkar ɗan makaɗi, sai su dinga ba da amo, su kuma suna taruwa suna rawa (Salihu, 1985:1). Kiɗa ya zama ɗan kabar tsaka a rayuwar Hausawa, baya ga lokacin cin abinci da ibada da karatu, da wuya a sami wani aiki da Bahaushe yake yi wanda babu kiɗa a cikinsa (Gusau, 2008:55).

Ma’anar Kiɗa:

Kiɗa shi ne samar da wani sauti na musamman ta hanyar goga wani abu ko busa shi ko girgiza shi ko buga shi ko ƙyanƙyasa shi kuma ya zamanto sautin da aka samar yana da manufa (Dumfawa, 2016). Shi kuma Zarruq da wasu (1987) suna ganin cewa, “Kiɗa yana nufin wanzar da daddaɗan amo daga abubuwan bugawa ko na gogawa ko na busawa ko kuma na girgizawa.”

Kiɗa abu ne da ake gwama abubuwa biyu su bayar da wani amo, inda ake haɗa misali baki + ƙahon dabba, ko dutse + dutse, ko tafi + tafi, ko ganga + gula ko makaɗi da sauransu. Haka kuma duk da yake ana yin kiɗa don wata manufa, kiɗa yakan shiga jikin mai sauraro, ya sa masa karsashin da har za ta kai ya dinga rausayawa yana tattakawa (Gusau, 2008:54).

Daga waɗannan bayanai na masana za mu iya cewa buga abubuwan bugawa ko ƙyanƙyasa abubuwan ƙyanƙyasawa ko girgiza abubuwan girgizawa ko busa abubuwan busawa ko goga abubuwan gogawa, kuma abun ya samar da amo mai wata manufa, tare da sa karsashi, shi ake kira da kiɗa. Haka kuma duk wani abu da yake samar da wancan amo idan an sarrafa shi, to shi ake kira da kayan kiɗa.

Misalan wasu daga kayan kiɗan Hausawa sun haɗa da kotso da kalangu a nau’in bugawa, molo da garaya a yanayin gogawa, kwamsa da kacakaura a fasalin girgizawa, algaita da farai a farfajiyar busawa, sai kuma kuge da ruwan gatari a fagen ƙyanƙyasawa. Tun da yake haka ne, yanzu sai mu duba wasu daga cikin kayan kiɗan nan mu bayyana yadda suke da yadda ake amfani da su da kuma ajin makaɗan da kan yi amfani da su.

Bayanin wasu daga cikin kayan kiɗan Hausawa

  1. Kotso ko Toho
    Kotso abin kiɗan Hausa ne wanda yake bi wa taushi, sai dai bai kai asalinsa ba, domin taushi ba a kaɗa wa kowa shi sai ɗan jinin sarauta, amma kotso ana iya kiɗan game-gari da shi ba tare da darajarsa ta faɗi ba (Gusau, 2008:83). Siffar kotso kamar ta kalangu ce, sai dai ana yi masa bakuna biyu ne, sama da ƙasa. Saman ake rufewa da fata mai kyau, sannan a yi wa ƙasan tsawon wutsiya kuma a bar shi a buɗe. Ana sassaƙa shi daga itacen madobiya ko aduwa ko ƙirya ko marke ko ɗinya da sauransu. Ana rufe shi da fata a yi wa gefensa ƙangu ko boya, a ɗaure ta da zare (tsarkiya), sannan a tanke jikinsa da zaren tsarkiya (Gusau, 2008:84). Kenan dai ana yi masa baki ɗaya ne, a rufe sama da fata a bar ƙasa buɗe, sai dai ana yi wa ƙasan hudoji don ɗaura zaren tsarkiya, sannan a ja ta zuwa sama inda fatar take a tanke. Ana manna danƙon nike a kuma shafe fararren itacen da man gyaɗa ko na shanu don ya qara zaƙi da amo. Da hannu ake kaɗa kotso, ta amfani da yatsu ko tafin hannun, wato ba a kaɗa shi da gula ko ɗan makaɗi. Daga cikin makaɗan kotso akwai shahararru irin su Musa Ɗanƙwairo Maradun da Abdu Kurna da Ibrahim Ɗanmarayan Kotso Daura da Budan Zakka da Ibrahim Narambaɗa da sauransu. Mafi akasarin masu kiɗa da kotso za a iske makaɗan sarauta ne.
  2. Kuwaru
    Kuwaru na ainahi shi ne wanda makaɗan noma suke amfani da shi, wasu daga cikinsu ne suka juya suna aiki biyu da shi, wato kiɗan noma da na sarauta (Gusau, 2008:85). Ana yin kuwaru da kore, wato sassaƙaƙƙen itacen ƙirya ko kawo ko madobiya ko marke da makamantansu. Ana fafare tsakiyar sannan a rufa shi da fatar akuya. Daga saman fatar za a sa zare, wato zaga da za ta ratsa ta, a gefe ɗaya kuma za a manna danƙon nike.

Kuwaru yana da kama irin ta kalangu, sai dai ya fi shi faɗin ciki kuma daga ƙasansa ba a rufe yake ba. Za a gewaye gefen saman kuwaru da ƙangu ko boya a ɗaure da zare, sannan kuma ana rufe shi da fata ta akuya wadda za ta kame shi tamau ta game sosai. Idan aka buga kuwaru yakan ba da sauti kamar dam-dam-dam ko tim-tim-tim (Gusau, 2008;86).

Shi ma kuwaru ana kaɗa shi ne da tafin hannuwa, sannan sautinsa ya danganta da yadda makaɗin ke matse shi a yayin kaɗawa. Daga cikin makaɗan kuwaru sun haɗa da, Alhaji Abubakar Akwara Sabon Birni da Jibo Magajin Kuwaru Gwadabawa da Alhaji Abu ɗankurma Maru, waɗanda duk suna da iyayen gida sarakuna.

  1. Kuntuku/Turu/Kuntukuru/Kurkutu
    Wani abun kiɗa ne mai fasali irin na dundufa (Gusau, 2016:21). Ana yin kuntuku da ita ce kamar su ƙirya da ire-irenta, a sassaqe itacen a yi masa siffar akushi, a yi masa baki mai ɗan faɗi a sama, a ƙasa kuma a tsuke shi, kuma ba a buɗe ƙasan take ba. Za a rufa bakin (saman) da fatar akuya a ɗaure gangar jikin da tsarauki ko zare mai ƙarfi. Ana kaɗa kuntuku ne da gula ba mai lanƙwasa irin na kalangu ba. Sannan akan haɗa shi da kayan kiɗa kamar kalangu domin su tashi amo wanda zai ba da armashi. Ana girka shi a ƙasa ko a matse shi a tsakanin cinyoyi a yayin kaɗa shi.
  2. Gurmi
    A yayin haɗa gurmi za a sami ƙoƙo na duma ko na ƙwarya, sai a rufa shi da fatar damo ko guza. Daga nan sai a sami itacen ɗunɗu gwargwadon tsayin da ake buƙatar ya kasance, a sako shi a cikin ƙoƙon. Sannan a sami izgar doki a ɗaura a jikin itacen a sama da ƙasan ƙoƙon. Wasu daga cikin kayan haɗa gurmi su ne duma da fatar damo ko guza da izgar doki ko tsarkiya da itace, ana kuma taɓa shi da hannu ko wani ɗan tsinken itace ya rinƙa ba da sauti mai ziza, kamar girin-girin-girin… Makaɗan game-gari ne suka fi amfani da gurmi a wuraren bukin suna ko aure ko sana’o’I, wani lokacin ma ana kiɗan bori da shi. Misalin makaɗan gurmi sun haɗa da Ali Makaho da Alhaji Musa Gumel da Bahausa Maigurmi da sauransu da yawa.
  3. Kumsa/Kwamsa
    Kumsa ko Kwamsa wani abun kiɗa ne da ake yi da fatar dabba ko ƙwaro irin su Damo ko Tsari ta hanyar aza fatar a kan wani mariqin gora/komo/jemo na duma, amma ƙarami, a haɗa da yazga/yizga ta doki ko zaren lilo mai ƙwari daga farkon ƙoƙon ya zuwa ƙarshensa, domin idan aka goga masa zobe ko wani itacen da aka feqe mai ƙwari (kamar itacen da ake tsiren nama da shi) zai fitar da sautin da ake buƙata
    Kumsa/Kwamsa ƙarama ce sosai, domin ba ta kai girman Kuntigi ko molo ba. Akasari akan fara sabgar goge ne da ita, kafin a ɓuge ya zuwa amfani da Kuntigi da Kukuma da Molo.

A cikin shekarun 1960s zuwa 1970s an yi ta amfani da gwangwanin kifin sadin, wanda aka cinye kifin da ke cikinsa, wajen haɗa wannan abun kiɗa da ake kira Kumsa/Kwamsa. Marigayi Alhaji Hassan Wayam mai goge/kukuma ya soma wannan sabga ta kiɗa da waƙa ne da wannan abun kixa, wato Kumsa/Kwamsa tun lokacin da yake qauyensu da ke yankin Maradun a Jihar Zamfara, kafin daga bisani ya tanadi Kukuma (Birnin-magaji, 2022- bayani ta manhajar WhatsApp).

KAMMALAWA

Wannan aiki ya bayyana yadda kiɗa ya samu a duniya ta silar neman abinci a farauta da kuma buwaya a yaqe-yaƙe, daga bisani Hausawa suka fara amfani da ƙaho a matsayin kayan kiɗa na farko-farko domin sadarwa har zuwa inda suka fara amfani da dutse domin nishaɗin rayuwa. An bayyana ma’anar kiɗa, inda masana suka ɓarje nasu gumi, daga baya muka fahimci lallai kiɗa shi ne buga wani abu ko busawa ko karkaɗawa ko girgizawa da makamantan haka, domin samar da wata manufa ko sanya karsashi da nishaɗi.

Mun kawo bayanin wasu daga cikin kayan kiɗa kamar kotso da kuwaru, waɗanda ake bugawa da tafin hannu, kuma mafi akasari makaɗan sarauta ke amfani da shi. Sai kuma kuntuku da ake bugawa da gula ko ɗan makaɗi, wanda makaɗan game-gari ke haxa shi da wasu kayan kiɗan domin armasawa.

Daga ƙarshe mun ga yadda gurmi da kumsa suke, wato abin kiɗa nau’in izga ko tsarkiya da akan kaɗa su da zobe ko ɗan ƙaramin itace mai ƙarfi.

Manazarta:

Dumfawa A. A. (2016). Laccar aji ta ALH 404. Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka Na Hausa; Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Kano-Nigeria: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2016). Ƙamusun Kayan Kixan Hausa. Kano-Nigeria: Century Research and Publishing Company Limited.
Ibrahim, M. S. (1983). Kowa Ya Sha Kiɗa. Lagos-Nigeria: Longman Nigeria PLC.
Salihu, A. A. (1985). “Kaɗe-kaɗen Hausawa da Bushe-bushe da Kayan yin su.” Makon Hausa na 13. Kano: qungiyar Hausa, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Zarruq R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. Ibadan-Nigeria: University Press PLC.
Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin-magaji: Bayani ta manhajar WhatsApp a ranar 20 ga Disamba, 2022.