Ya kamata hukuma ta kawo ƙarshen masu tallan jabun magungunan kashe ƙwari – A.A Na Mazadu

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA ABKANO

An sake jaddada buƙatar da ke akwai ga shuwagabannin haɗaɗiyar gamayyar masu sayar da magungunan kashe ciyayin da ke hana amfanin gona sakat da magance yawaitar yaɗuwar ƙwari masu kashe amfani, dake kasuwar Abubakar Rimi, Kano, da su yi wani abu da zai kawo ƙarshen babbar matsalar nan ta sayar da jabun magungunan kashe ƙwari , da lamarin ke neman ɓata wa ‘ya’yan ƙungiyar suna.

Aminu isyaku A.A na mazadu, ɗan kasuwa dake sayar da magungunan kashe ƙwari da illata amfanin gona a rukunin masu sayar da maganin kashe ƙwari a babbar kasuwar Abubakar Rimi da ke Kano, shi ne ya bayyana hakan cikin hirarsa da manema labarai, kamar yadda ya ce a matsayinsa na wanda ya gaji ita wannan sana’a ta sayar da mugungunan kashe ƙwari, bai tava cin karo da ƙalubale ba na wasu ko wani su kawo masa koken na sun sai kaya a wurin sa marar kyua, kamar yadda waɗansu ke sayar da jabun magungunan kashe ciyaye da ƙwari n da ke illata amfanin gona.

Inda ɗan kasuwar, Alhaji Aminu Isyaku, na mazadu, (A.A) Ya bayyana wannan matsala ta sayar da jabun magunguna, da wasu kan yi a wurare daban-daban da cewa ita ce, babbar matsalar da ta fi damun su, wato a matsayin su na tsofin ‘yan kasuwa, musamman a kasuwar ta Abubakar Rimi, Kano, da akasari ake yi wa ƙungiyar tasu kuɗin goro.

Alhaji Isyaku Aminu Na Mazadu daga bisani ya yaba wa kafanoni, dake samar da magungunan, dake jahar kano, da ma na Arewacin ƙasar nan bisa yadda suke samar musu da kayyakin cikin ƙanƙanin farashi, ta yadda su ma za su yi wa sauran al’umma sauƙi, duba da yadda aka tsinci kai a wani ƙadami na tsadar rayuwa.