Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rahotanni da ga Jihar Neja na bayyana cewa wasu ɓatagari sun tare tireloli maƙil da kayan abinci a yankin Suleja, lamarin da ya sa sojoji suka yi harbi sama don korar su a jiya Alhamis.
Wani ganau, Alhassan Abdullahi, ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa ɓatagarin, wanda suka ƙona tayoyi sun tare tirelolin da ke tahowa daga Abuja zuwa Kaduna.
Ya ce sun sace buhunan kayan abinci iri-iri, musamman shinkafa kafin sojoji su isa wurin.
“Allah Ya sanya sojoji sun isa wurin sannan suka fara harbin bindiga a iska don tsoratar da ɓatagarin. Amma ko da hakan, da yawa daga cikinsu sun tafi da buhunan shinkafa da katan-katan na taliya da sauran kayan abinci.”
Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da wahalhalun da ƙasar ke fama da shi wanda ya haifar da zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar.
