10
Aug
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumomin kasuwar hatsi ta ƙasa da ƙasa ta Dawanau da ke ƙaramar Hukumar Dawakin Toda a jihar Kano sun ɗauki wani kwakkwaran mataki na tabbatar da tsaron kasuwar ta hanyar shigar da ƙarin jami’an tsaro sama da 800. Shugaban ƙungiyar kasuwar, Alhaji Muntaka Isa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Litinin cewa matakin zai kare kasuwar yadda ya kamata daga ɓarna da sata. Isa ya bayyana ƙoƙarin haɗin gwiwa na sojojin Nijeriya, 'yan sanda, da hukumomin tsaro na jihohi, wanda ya ƙara inganta harkar tsaro…
