Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya bayyana rashin jituwa tsakanin matatar mai ta Aliko Dangote da Hukumar Haƙowa da Sarrafa ɗanyen Mai ta Nijeriya (NMDPRA) a matsayin abin damuwa.
A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na ɗ a ranar Talata, Atiku ya bayyana matatar Dangote a matsayin babbar hanyar zuba jari mai zaman kanta a ƙasar wanda ke da muhimmanci ga tattalin arzikin Njeriya.
Atiku ya ce, kare manyan jari kamar matatar mai ta Aliko Dangote da ke Legas na da matuƙar muhimmanci wajen jawo hannun jarin ƙasashen waje zuwa cikin ƙasar, yana mai cewa “babu wani mai saka hannun jari da zai aminta da ƙasar da ta lalata manyan kadarorinta.”
“Matatar man mai nauyin bpd 650,000 na da matuƙar muhimmanci ga buƙatun makamashi da haɓaka tattalin arziki, kuma jarin NNPCL ya nuna muhimmancinsa.
Idan muka yi watsi da wannan, za mu yi kasadar daƙile muhimman saka hannun jari kai tsaye daga ƙetare,” inji shi.
