Ingancin man dizal ɗinmu daidai yake da na sauran duniya – Matatar Ɗangote

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Matatar Ɗangote ta sake tabbatar da cewa man dizal ɗin nata yana da inganci idan aka kwatanta da na ƙasashen waje da ake shigowa da shi, kuma ya cika ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne dangane da kalaman da babban jami’in hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa, NMDPRA, Farouk Ahmed ya yi a baya-bayan nan, cewa ingancin man dizal ɗin ya yi ƙasa da wanda ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

An ruwaito matatar ta ce, babu ɗaya daga cikin man dizal da ake shigowa da shi Nijeriya da zai iya yin gogayya da na matatar Dangote ta fuskar inganci, kuma duk wani ƙwararre da ke da niyyar gwada kayayyakinmu da waɗanda ake shigo da su kai tsaye zai iya tabbatar da hakan.

Babban jami’in kasuwanci na rukunin Dangote, Rabiu A. Umar ne ya bayyana haka ranar Juma’a a Kano a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai.

“Ingantacciyar dizal ɗinmu na iya tsayawa gwajin lokaci a ko ina cikin duniya, mun fara da 600-700 PPM saboda sabuwar samfuri ne.

“Yanzu, samar da mu yana kan 87 PPM, kuma a karshen watan Agusta, zai kasance a 10 PPM.

A cewarsa, ko a lokacin da shugabancin majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya ziyarci matatar ne a ƙarshen makon da ya gabata, a kan hanyarsu ta sayo man dizal daga gidajen mai guda biyu, idan aka kwatanta da na matatar man Dangote; sun yi mamakin sakamakon ingancin samfuranmu.

“Gwajin da aka gudanar a gabansu ya tabbatar da ingancin man dizal ɗin namu kuma ya tabbatar da cewa dizal ɗin namu na daya daga cikin mafi inganci a duniya da ƙarancin sinadarin sulfur,” inji Umar. 

By ukarofi