Daga MAHDI M. MUHAMMAD
ƙungiyar Masu Kiwon Kaji ta Nijeriya (PAN), reshen Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta buƙaci gwamnatin tarayya da hukumar Abuja da su taimaka wa mambobin da bala’i ya shafa domin farfaɗo da sana’o’insu.
Pius Aminu, Shugaban PAN, reshen babban birnin tarayya, ya yi wannan roƙo a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) a Abuja ranar Talata.
Aminu ya ce, gyara masu kiwon kaji zai kare masana’antar daga durƙushewa.
Idan za a iya tunawa, guguwar ruwan sama ya lalata wasu gidajen kiwon kaji a ƙananan hukumomin Kuje da Kwali a Abuja, a lokacin daminar bara.
Shugaban wanda ya yi ƙarin bayani kan halin da masana’antar ke ciki a Abuja, ya ce har yanzu ƙungiyar ba ta samu wani ɗauki daga gwamnati ba.
A cewarsa, ya kamata gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta-ɓaci a harkar kiwon kaji domin ɗaukar matakin gaggawa kan halin da ake ciki.
“Lokacin da aka samu ambaliya, mutane duk sun yi ƙaura zuwa wurare daban-daban; wasu a makarantun firamare ana ba su katifu da kayan abinci.
“Amma idan ana maganar fannin kiwon kaji, an yi watsi da shi. Guguwar iska bala’i ce ta daga Allah, don haka ya kamata a yi la’akari da masana’antar.
“Muna kira ga gwamnati da ta kuma duba masana’antar. Haka kuma iskar ta shafi gonaki da yawa ta haka, ta rage yawan gonaki a Abuja, ya kamata a yi la’akari da masu kiwon kaji tare da ba da fifiko,” inji shi.
Aminu ya ci gaba da cewa, rugujewar gonakin ya ƙara yawan rashin aikin yi a yankin, tun da aka mayar da waɗanda suka yi aiki a gonakin da abin ya shafa zuwa kasuwar kwadago.
Shugaban PAN ya bayyana cewa kawo yanzu, manoman kaji ba su samu wani tallafi ba.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kai wa manoman agajin kuɗi da sauran su, domin su samu damar sake gina sana’arsu da kuma ci gaba da kiwon.
Ya ƙara da cewa, masu gonakin da abin ya shafa ba su samu damar sake ginawa ba saboda rashin kuɗi.
