Gidauniyar Alheri Danƙo Ne ta ba da taimakon ruwa a wasu unguwannin Jos

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos

A sakamakon yadda ake fama da matsanancin zafi da ƙarancin ruwa a wasu sassan garin Jos, wata ƙungiya mai tallafawa mabuƙata mai suna Alheri Danƙo Ne Charity Foundation ta taimaka da tankar ruwan famfo ga mazauna Anguwar Rogo da Anguwar Rimi, domin sauƙaƙa musu wuyar da suke sha ta rashin ruwan famfo, da tsadar wanda ake saya a wajen masu kura.

Shugabar ƙungiyar, Hajiya Farida Shehu ta bayyana cewa, wani bawan Allah ne ya taimakawa ƙungiyar da kuɗin sayen wannan ruwa, sakamakon koken da ƙungiyar ta kai masa da buƙatar taimakawa jama’ar wannan yanki, da ke fama da ƙuncin rashin ruwa, duk kuwa da azumin da ake yi, cikin matsanancin zafin rana.

Ta ce, “Ganin halin da jama’a suke ciki na wahalar ruwa ya sa muka bazama neman wanda zai taimaka mana da kuɗin da za mu saya musu ruwa, don mu raba kyauta saboda Allah.’

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da wannan tallafi na ruwa, sun yi matuƙar godiya ga waɗanda suka taimaka musu, inda suka bayyana cewa sun jima cikin wannan mawuyacin hali na rashin ruwa, saboda rashin ruwan famfo da ƙafewar rijiyoyi, da kuma tsadar ruwan sayarwa na bohol wanda da ƙyar ake samunsa.

Wata mata da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa, suna sayen kurar ruwa tsakanin Naira 700 zuwa 1000, wani lokaci kuma tun tsakar dare suke fita da yaransu neman ruwa har zuwa asuba kafin su samo wanda za su yi aiki da shi.

Tun da aka fara azumin watan Ramadan na bana, ƙungiyar Alheri Danƙo Ne Charity Foundation tana ciyar da mutane aƙalla 600 da dafaffen abincin buɗe-baki a kowacce rana, banda mutane 400 da aka rabawa ɗanyen kayan abinci.

By ukarofi