Daga JOHN D. WADA a LAFIYA
Sabon shugaban ƙungiyar ’yan adaidaita sawu na ƙaramar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa, Kwamaret Abba Gana Ali da aka fi sani da ɗan Borno, ya alaƙanta biyayya da tsari da kuma nasarori da ake samu a yanzu haka tsakanin mambobin ƙungiyar masu harkar adaidaita sawu, wadda ake kira keke-napep a Turance na ƙaramar hukumar ta Karu a jihar ga yadda sabon shugabancin ƙungiyar na yanzu a aarƙashin jagorancinsa ke ɗaukar kwararan matakan hukunci ba tare da ɓata lokaci ba akan duk mamban da da an samu da laifin karya dokokin ƙungiyar.
Shugaban Kwamaret Abba Gana Ali wanda aka zaɓa kwanakin baya a matsayin sabon shugaban ƙungiyar na yankin Karu ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu a ofishin ƙungiyar da ke Ado a aaramar hukumar a aarshen mako da ya gabata.
Ya ce, ba shakka kafin yanzu kowa yasan yadda wasu miyagun ’ya’yan ƙungiyar ke cutar da fasinjojin su tareda haɗa baki da wasu miyagun mutane ana cin zarafin al’umma ba gaira ba dalili ta kwace musu dukiyoyin su da sauran su.
Shi ya sa acewar sa da zuwansa kujera a matsayin sabon shugaban ƙungiyar na shiyar ya cigaba da ƙirƙiro tare da aiwatar da wasu sabbin tsare-tsare musamman na hukunta ire-iren miyagun mambobin nasu da ke taka dokokin, inda ya cigaba da bayyana cewa, “Kaga shiyasa nake so inyi amfani da damar nan in sanar da kai kuma cewa an yi ta samun waɗannan munanan dabi’u tsakanin wasu mambobin namu amma a yanzu da yardar Allah da kuma ire-iren sabbin matakan na hukunci da muke ɗauka a wasu lokutan ma harda bulala muke yin amfani da shi mu kawo mamba daya karya doka nan ofishin mu mu zane shi don hakan yakasance darasi ga wasu,” inji shi.
Sabon shugaban ƙungiyar wanda matashi ne Kwamaret Abba gana Ali ƙan Borno ya kuma yi amfani da damar inda ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Karu Thomas James dangane da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin su, inda ya ce hakan yana bunƙasa harkokin ƙungiyar a shiyar akoyaushe.
A ƙarshe, sai matashin ya kuma yi amfani da damar, har ila yau inda ya yaba wa duka mambobin sa dangane da haɗin kai da biyayya da kuma goyon baya da suke nana wa shugabannin ƙungiyar a yanzu inda ya kuma buƙaci gwamnatoci a duka matakai su riƙa tallafa musu a ƙungiyar ce don rage musu wahalhalu da suke fuskanta a yanzu kamar kowa sakamakon tsadar rayuwa.
