Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta dakatar da haraji kan kayayyakin abinci da ake shigowa da su ƙasar.
Hakan ya fito ne a wani faifan bidiyo da shugaban hukumar kwastam, Bashir Adewale Adeniyi ya wallafa a shafin X, inda ya ce an dakatar da shi ne domin bai wa ‘yan Nijeriya damar samun wadataccen kayan abinci.
Ya ƙara da cewa, hauhawar farashin kayayyaki a duniya yana shafar ƙasashe ciki har da Nijeriya, yana mai cewa hukumar ta himmatu wajen aiwatar da umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da haraji kan muhimman kayayyaki.
“Hauhawar farashi a duniya yana shafar ƙasashe a duniya ciki har da Nijeriya. Domin magance hakan, gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kwastam ta Nijeriya na dakatar da harajin shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje da kuma haraji kan muhimman kayan abinci domin samun sauƙi.
“Mun himmatu wajen aiwatar da wannan matakin ba tare da wata matsala ba domin magance matsalar yunwa a ƙasarmu. Mun daidaita hanyoyin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje domin tabbatar da cewa kayayyakin Nijeriya sun isa kasuwannin duniya yadda ya kamata.”
Shugaban Kwastam ɗin ya yi gargaɗin cewa taɓarɓarewar hanyoyin samar da kayayyaki za ta shafi zuba jari daga ƙasashen waje, da gurɓata harkokin kasuwanci, da ƙara rura rashin zaman lafiya, da ƙara ƙarancin kuɗi da kuma kawo cikas ga tara kuɗaɗen shiga.
A halin da ake ciki, Hukumar Kwastam ta ce ta zarce adadin kuɗaɗen shigarta na rabin farkon shekarar 2024.
Duk da cewa ma’aikatar ta samu kuɗin shigar da ya kai Naira Tiriliyan 2.54, amma ta samu ribar tiriliyan N2.74, wanda ya zarce kashi 8 cikin ɗari, kuma ya nuna ƙaruwar kashi 127 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Jami’in hulɗa da jama’a na NCS, Abdullahi Maiwada, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin yayin da yake bayar da rahoton ayyukan hukumar na tsakiyar shekara.
