Yadda za ku buɗe layukan wayarku ba tare da zuwa kamfani ba

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

ƙungiyar masu kamfanonin wayar ta bayyana yadda mutanen da aka rufe wa layukan za su iya buɗe su.

A cikin sanarwar, ta ce mutane na iya amfani da hanyar latsa wasu lambobi domin haɗa layulan su da lambar Shaidar ɗan ƙasa don tantance matsayin layukansu da kuma buɗe su.

Sai dai sanarwar ta ce idan har aka kasa buɗe layi ta hanyar amfani da lambobin, mutane za su iya zuwa ofisoshin kamfanonin waya domin kai ƙorafi.

An wari gari galibin masu amfani da layukan MTN da 9mobile ba su iya kira tun daren Asabar.

Wannan lamarin na zuwa ne kwanaki kaɗan gabanin wa’adin ranar 31 ga Yuli, 2024 da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta sanya. 

Bayanai daga Hukumar sadarwa ta Nijeriya sun nuna cewa akwai masu amfani da wayar hannu miliyan 219,005,878 a ƙasar.

A watan Fabarairun 2020 ne gwamnatin tarayyar Nijeriya ta umurci hukumar sadarwa ta ƙasar (NCC) da hukumar rajistar ’yan ƙasa ta NIMC su fara aikin haɗa duk wani layin waya da lambar zama ɗan ƙasa.

Gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa za a ɗauki matakin rufe duk wani layin waya da ba a haɗa shi da lambar zama ɗan ƙasa.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yunƙuri na shawo kan matsalolin tsaro.

Al’ummar ƙasar sun sha kokawa kan yadda masu aikata laifuka, musamman masu garkuwa da mutane ke amfani da layukan waya wajen karɓar kuɗi daga hannun ’yan uwan waɗanda suka yi garkuwa da su.

Yadda za ku buɗe layin MTN daga wayarku ba tare da zuwa ofishinsu ba:

Kamfanin sadarwa na MTN a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya bayyana yadda masu amfani da layin za su iya buɗe layinsu.

Ya ce; latsa lambobin – *996*lambar NIN#

A Airtel kuwa, ana sa ran abokan cinikin Airtel su danna *121# sannan su shigar da lambar NIN goma sha ɗaya, sai #.

Ga Glo kuwa, lambar ita ce *109*NIN lamba#.

By ukarofi