Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja
Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta buƙaci ‘yan jarida, waɗanda za su fito filin dagar zanga-zangar matsin rayuwa da ake gudanar da su tabbata sun sanya riguna mai ɗauke da alamar aikinsu a lokacin fitowarsu.
Wannan sanarwa ta fito daga bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Abuja, S. Josephine Adeh, a yammacin Lahadi.
Sanarwar ta ce, “Kwamishinan ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ya umarci ƴan jarida da za su fito aiki ranar Litinin, domin ɗaukar yadda zanga-zanga za ta wakana, da su sanya kayan gidan jaridarsu, sannan su tabbatar suna da katin shaida.”
Idan za a iya tunawa, a jiya ne Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) ta yi ƙorafi kan zargin cin zarafin ‘yan jarida da jami’an tsaro suka yi a lokacin wannan zanga-zanga.
