Sanatan Zamfara ya raba taki ga manoma 3,000

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sanata Sahabi Ya’u mai wakiltar mazaɓar Zamfara ta Arewa ya sayo tirela huɗu na takin zamani ga manoma dubu uku a mazaɓarsa.

Sanata Sahabi Ya’u yayin da yake ƙaddamar da rabon takin a garin ƙaura Namoda, hedkwatar ƙaramar hukumar ƙaura Namoda a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana cewa takin da ya samar kyauta ne.

A cewarsa kowace ƙaramar hukumar ƙaura Namoda, Shinkafi, Birnin Magaji da Zurmi domin amfana da babbar mota ɗaya.

Ya ci gaba da cewa, za a raba buhunan taki iri-iri guda 500 ga manoma marasa galihu yayin da za a raba buhu 100 a tsakanin shugabannin jam’iyyar APC na kowace ƙaramar hukuma ta mazaɓarsa.

Sanata Ya’u ya bayyana cewa, kowane manomi zai bada ƙarin kayan masarufi kyauta domin bunƙasa nomansa.

Ya kuma buƙaci kwamitin da ke gudanar da rabon tallafin domin tabbatar da cewa manoma na gaskiya ne kawai aka bai wa takin, ya kuma buƙace su da su tabbatar da adalci a lokacin rabon.

Dangane da matsalar rashin tsaro da jihar ke fama da ita, Sanata Sahabi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na aiki ba dare ba rana domin ganin an dawo da zaman lafiya a jihar.

“Shugaba Tinubu yana da cikakkiyar masaniya kan matsalar rashin tsaro da ke addabar jiharmu da sauran jihohin Arewa maso Yamma kuma gwamnati na bakin ƙoƙarinta wajen ganin an daƙile ta’addanci a jihar da sauran jihohin Arewa maso Yamma.”

Ya buƙaci al’ummar jihar da su kasance masu bin doka da oda tare da marawa gwamnati baya a ƙoƙarinta na ganin an samu zaman lafiya a jihar.

Hakazalika, Sanata Sahabi Ya’u ya bayyana cewa tattaunawa ce kawai mafi kyawun zaɓi tsakanin gwamnatin tarayya da matasan da suka ji haushin waɗanda suka shirya zanga-zangar a faɗin ƙasar.

“Ba wai ina bayar da shawarar zanga-zanga ba ne amma ina bayar da shawarar a tattauna da matasanmu da gwamnatin tarayya a matsayin hanya ɗaya tilo da za ta hana su gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan kan matsalolin tattalin arzikin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a ƙasar nan,” Sanata Ya’u ya ce. 

Ya kuma yi kira ga matasan Nijeriya da su janye shawarar da suka yanke su rungumi tattaunawa ta hanyar miƙa buƙatunsu ga gwamnatin tarayya domin ta ɗauki matakin gaggawa.

By ukarofi