Bayan shafe kwanaki ana zanga-zanga a faɗin ƙasa, abubuwa sun tsaya da dama a ƙasar musamman al’amuran kasuwanci.
Zanga-zangar yunwar a na sa rai za a ƙare ta 10 ga watan Agusta 2024. Zanga-zangar da ta fara a mastayin ta lumana ta canza salo ta koma rikici musamman a garuruwan Kano da Kaduna.
A Kaduna, bankuna da kasuwancin ya fara dawowa dai dai bayan rage dokar hana zirga-zirga da aka sanya a Kaduna da Zaria.
Kasuwar Central Market ta Kaduna ta samu masu siyayya sun fito da dama domin sayen kayan abinci da sauran kayan masarufi.
A Kano kuwa, nan ma Zanga-zangar ta rikiɗe ta zama rikici nan ma. Inda aka samu rahotannin sace-sace, da fasa shagunan mutane.
Mabarata da karuwai sun koka kan yadda zanga-zangar ta sanya su cikin wani halin babu. Su na roƙon masu zanga-zangar da su haƙura haka.
Baba Halliru wani maroƙi daga Rijiyar Zaki ya bayyanawa kamfanin dillancin Labarai na Nijeriya cewa yana cikin wani halin ƙunci da yawa saboda wannan zanga-zangar. Ya bayyana kwanaki kenan ba a ci abinci a gidan shi ba saboda wannan zanga-zangar.
Haka mabarata daga sassa daban-daban na jihar su ka bayyana.
Haka ma karuwai ba a bar su a baya ba, inda wata mai suna Monica James da ke aikinta a France Road tace a zo a yi sulhu da masu zanga-zanga domin shine kaɗai mafita. Ta bayyana cewa babu kwastomomi kwanakin nan.
Haka ma sauran karuwai a sassa daban daban-daban na sabon gari kamar su Enugu Road, Yoruba Road da sauran sashen Sabon Garin da ke Kano.
Bayan buɗe kasuwannin kano, an samu hauhawar farashi sosai a kasuwar Singa da Dawanau.
