Majalisar Dattijai za ta binciki gwamnatin Buhari bisa kashe Dala biliyan 1.5 a gyaran matatar Fatakwal

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI a Abuja

Majalisar Dattijai ta nuna damuwarta kan yadda aka kashe Dala biliyan 1.5 wajen gyaran matatar mai ta Fatakwal lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a shekarar 2021 ba tare ganin abin a-zo-a-gani ba.

Sanata Opeyemi Bamidele, wanda shi ne shugaban kwamitin musamman kan yin zargin zagon ƙasa ga tattalin arziki a fannin man fetur na Nijeriya, ya koka game da hakan ne a lokacin tattaunawa da masu-ruwa-da-tsaki a ranar Laraba a Abuja.

Mista Bamidele, wanda kuma shi ne Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, ya ce, ba daidai ba ne a riƙa wasarairai da kadarorin al’umma alhali a na tattalin kasuwancin ƙashin kai kuma a na bunƙasa shi.

Ya tuno da yadda Majalisar Zartarwar, FEC, ta tabbatar da shirin Ma’aikatar albarkatun man fetur na yin gyaran matatar Fatakwal akan Dala biliyan 1.5, ya na mai nuna damuwa kan rashin kula da matatun jihohi da na ƙasa duk da maƙudan kuɗaɗen da ake warewa don ba su kulawa yadda ya dace.

“Nijeriya ta na fuskantar yanayi na ƙalubale. Samarwa da raba tataccen man fetur su na samun cikas a wannan lokacin a ƙasar”, inji shi. Ya ce tsawon layuka a gidajen mai zasu tabbatar da haka.

Ya ƙara da cewa, wani ƙarin abin takaicin shi ne shigowa da gurɓatattun dangogin man fetur da na gas zuwa Nijeriya.

Bugu da ƙari, ya ce gwamnati ta zuba biliyoyin daloli domin kula da kuma dawo da martabobin matattun man fetur na ƙasa a Kaduna, Fatakwal da kuma Warri, waɗanda har yanzu ba sa aiki.

Daga ƙarshe, Sanatan ya ce sun shirya gudanar da bincike wajen ganin an gano bayanan haƙiƙanin dalilan da ke sabbaba hakan.

Sai dai, shugaban kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari ya ƙaryata zargin yin zamba cikin aminci a matatar ƙasa.

By Babaji