
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da shirin sayar da shinkafa kan farashi mai rahusa ga ma’aikata wanda haka na nufin janye batun bayar da umarni ga waɗanda ke buƙata.
Sanarwar ta fito ne daga wani sabon saƙo daga ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnati a ranar Alhamis.
Saƙon wanda ke ɗauke da sanya hannun Daraktan albarkatun al’umma, Aderonke Jaiyesimi, bai bayyana dalilan da su ka sanya aka janye batun ba.
Haka nan, babu gamsashshen bayani game da dakatarwa ce ta din-din-din ko kuma ta wucin-gadi, ta na mai kira ga sauran ɓangarori da su isar da sakon ga waɗanda al’amarin ya shafa.
A satin da ya gabata ne, ma’aikatar ta sanar da ma’aikatan da ke buƙatar sayan buhu shinkafa mai nauyin kg50 kan farashin Naira 40,000 daga gwamnati su cike shafin da ta bayar na yanar gizo inda ta yi iƙirarin yin adalci wajen sayarwar da kuma rabawa.
Haka nan, dakatarwar ta haifar da cecekuce a cikin al’umma, yayin da su ke jiran ƙarin bayani game da hakan.
