Gwamnatin Neja ta tallafa wa iyalan waɗanda ƙasa ta rufta da su

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Iyalan mutanen da ƙasa ta rufta da su a wajen wani haƙar ma’adanan ƙarƙashin ƙasa a jihar Neja sun samu tallafin Naira miliyan 50 daga gwamnatin jihar.

Tun kimanin watanni 2 da suka gabata kenan dai da ƙasa ta rufe waɗansu masu haƙar ma’adanai a yankin na Galadiman Ogo ta ƙaramar hukumar Rafi, da kawo yanzu aak lalubo gawarwakin mutane 10 sannan aka samu 8 da ransu inda har ya zuwa yanzu ake ci gaba da ƙoƙarin zaƙulu gawarwakin wasu mutane 4.

Sakataren gwamnatin jihar Nejan Alhaji Abubakar Usman ya  ce duk da yake kamfanin dake aiki a wannan wuri ya saɓawa ƙa’ida, gwamnati ta nuna jinƙai ne shi ya sa ta tausayawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa.

A yanzu dai an kafa wani kwamiti da aka bai wa mako biyu domin aikin tantance iyalan waɗannan mutane,

Alh. Umar Aliyu Bala Shine Hakimin yankin na Galadiman Kogo tun daga lokacin da lamarin ya faru babu wani tallafi da suka samu daga gwamnati sai yanzu, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano waɗanda har yanzu suke cikin ramin.

Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce har yanzu dokar hana haƙar ma’adanan ƙarƙashin ƙasa ba akan ƙa’ida ba tana aiki daram al’amarin da ta ce yana ɗaya daga cikin matakan da take ɗauka domin shawo kan matsalar rashin tsaro da ya addabi wasu yankuna na jihar.

By ukarofi