Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja
Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya fi fifita yankin arewacin Nijeriya a naɗe-naɗe mafi muhimmanci da gwamnatinsa ta yi kawo yanzu.
Shettima, wanda ke magana da manema labarai a maraicen jiya Alhamis, 8 ga Agusta, 2024, ya ce, ma’aikatu da hukumomin gwamnati, waɗanda za su fi amfanar yankin Arewa, Tinubu ya naɗa ‘yan Arewa su jagorancinsu ne.
Ya fara da cewa, a cikin ministoci guda 46, Tinubu ya bai wa Arewa guda 24, inda hakan ke nufin gabaɗaya yankunan Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu da kuma Kudu maso Gabas na da guda 22 kacal a tsakaninsu kenan.
Ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya ɗauki ma’aikatu da hukumomi mafi tasiri ga Arewa da ƙasar bakiɗaya ya damƙa su a hannun ‘yan asalin yankin.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayar da misali da ma’aikatu kamar na noma, tsaro, ilimi da kuma hukumomi irin su NITDA da NCC, waɗanda a yanzu tattalin arzikin duniya ya jirkita ɓangarensu ne na kimiyya da fasaha ta fuskar samar da aikjn yi da bunƙasar cigaba. Ya kuma ƙara da cewa, Tinubu ya ƙirƙiro sabuwar Ma’aikatar Kiwo, wacce a ganinsa ‘yan Arewa ne za su fi amfana da ita.
Daga nan sai Shettima ya yi nuni da cewa, babbar matsalar Arewa ita ce, rashin haɗin kan shugabanninta. Don haka ya yi kira da a haɗa hannu wajen cin moriyar abubuwan more rayuwa da Shugaba Tinubu ya kawo.
