Ba a tuhuma ta da laifin kisa – Hon. Doguwa ga Hon. Abdulmumini

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ɗan Majalisar wakilai, Alhasan Ado Doguwa ya ce babu laifi ko tuhumar kisa akan sa, ya na mai mayar da martani ga takwaransa na jam’iyyar NNPP, Abdulmumini Jibrin kan zargin da ya ke masa.

A wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannunsa, Doguwa ya ce, “bari na tabbatar da cewa, daga yau, ni Doguwa, babu wata kotu a Nijeriya da ke tuhuma ta da laifin kisa, hannu a laifin kisa.”

Ya ce, ya fuskanci bincike da tuhume-tuhume kan laifin kisa da dama amma ya fito ya na mai wanke kansa inda ya ce cibiyar bincike ta FCID Abuja za ta tabbatar da hakan.

Acikin takardar da aka wallafa a ranar 8 ga watan Agusta, 2024, Doguwa ya yi dogon jawabi game tuhumce-tuhumcen kisa inda daga ciki ya ke cewa ya na mai bayar da haƙuri ga mutanen da ke cewa ya share batutuwan ƙarya, ƙazafi da shashancin Abdulmumini Jibrin da ke wakiltar mazaɓar Ƙiru da Bebeji a kan sa, ya na mai cewa wannan shi ne karo na ƙarshe da zai tanka masa a matsayinsa na ɗaya daga cikin ƴan demokraɗiyyar da ke yi wa ƙasa hidima.

A kwana nan ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan batun inda ta buƙaci Jibrin da gwamnatin Jihar Kano su biya Doguwa tara ta Naira miliyan 25 kan ɓata masa suna a idon jama’a.

Sai dai, Doguwa ya ce a wani rikici da aka yi a mazaɓarsa a lokacin zaɓen shekarar 2019, an samu rasa rayukan mutane 7 na ƴan jam’iyyar PDP tare ƙone motoci 25 na Kwankwaso da magoya bayansa waɗanda ake zargin Jibrin da hannu a ciki wanda Doguwa ya ce har yanzu ba a kai ƙarshe a ƙarar ba. Ya ce Kwankwaso da Abba da kuma Madaki shaidu ne akan hakan.

By Babaji