Muna fuskantar ƙalubale a jagorancin kasuwar gwarin Illeoko a Legas – Mu’awuya Simoli

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas 

Wani babban mai faɗa a ji a kasuwar gwarin Illeoko ta Ƙaramar Hukumar Alimosho dake cikin birnin Ikko, Alhaji Mu’awuya Idris Simoli ya bayyana cewar shi da sauran shuwagabannin kasuwar ta gwarin Illeoko suna fuskantar manyan ƙalubale mai yawa a kasuwar da kewayenta gaba ɗaya.

Alhaji Mu’awuya Idris Simoli ya furta hakan ne a Legas a lokacin da yake zantawa da jaridar Blueprint Manhaja dangane da al’amuran da suka shafi harkokin kasuwancin gwari a Legas baki ɗaya.

Simoli ya ci gaba da labarta wa Jaridar Blueprint Manhaja cewar haƙiƙa tun daga wancan lokacin ya zuwa yanzu kasuwar ta Illeoko tana fama da matsaloli na gwamnati nan da can waɗanda suka haɗa da rufe kasuwar baki ɗaya da sauran matsalolin da suke fitowa daga ƙaramar hukumar su ta Alimosho akan waɗansu ‘yan dalilai marasa tushe ballantana makama.

Ya ce sai sun ta yin zirga-zirga zuwa ƙaramar hukumar su ta Alimosho da waɗansu ofisoshin, sannan gwamnatin jihar Legas sannan a buɗe masu kasuwar, a cewarsa sau ɗaya gwamnatin jihar Legas ɗin take yi masu haka

Ya ƙara da cewa ko a kwanan nan ma gwamnatin Jihar ta Legas ta ƙara rufe masu kasuwar haka kawai ba su san hawa ba ballantana kuma sauka.

Ya ci gaba da cewa wata babbar matsalar kuma ita ce wani babban Bayarabe mai kuɗi ya zo da waɗansu ma’aikata da ta karda shaidar cewa wata kotu ta mallaka masa rabin kasuwar a matsayin filin gidajen iyayensa ne aka mayar da shi kasuwa. Ya ce a yanzu haka dai maganar tana kotu ana ta cakusawa domin gano musabbabin faruwar al’amarin. Ya ce akan hakan yake ganin ya kamata ya isar da saƙonsa na yin kira da babbar murya ga gwamnatin jihar Legas data dubi Allah da Annabinsa ta yi masu adalci bisa ga la’akari da yadda suka mallaki wannan fili na kasuwa tsawon shekaru da yawa suna gudanar da harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.

By ukarofi