Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An yi kira ga al’ummar Arewa musamman Hausa/Fulani su haɗa kai a yi aiki tare domin cimma manufofi da za su bunƙasa kima da ci gaba da za a samu kyakkyawan makomar fita daga mawuyacin halin da ƙasar nan take ciki.
Ya ce idan aka duba yawanci abokan haɗakarmu na ƙasar nan ƙabilu daban-daban kansu a haɗe yake amma Hausa/Fulani mu ba abinda yake a gabanmu sai biyan buƙatar son rai idan bamu sami haɗin kai ba ba za mu cimma ga ci ba.
Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass don haka a sa tsoron Allah a zuciya da neman gafararsa domin a samu kyakkyawar makoma, amma idan muka ci gaba da tafiya a ware a rarrabe za mu zama koma na baya.
Ya ce idan aka yi duba da matsalar harkar tsaro ta lalace da ta shari’a da tattalin arziƙi na ƙasa da kasuwanci sun lalace kuma Arewa tafi cutuwa da waɗannan matsalolin.
Gambo Ɗanpass ya ce yakamata a farka a yi karatun ta natsu a haɗa kai a yi tafiya ta nemawa al’ummar Arewa mafita da kawo ci gaba yadda za a kawar da dukkan matsaloli dake addabar ci gaban Arewa.
