Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gungun ‘yan bindiga sun arce da Sarkin Gobir, Isa Muhammad Bawa, wato Hakimin Gatawa da ke cikin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
An yi garkuwa da shi tare da ɗan sa da kuma ƙaninsa, kamar yadda Kantoman Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, Garba Umar Kaba ya shaida wa Daily Trust cewa an yi garkuwa da su a ranar Asabar kusa da Kwanar Maharba, daidai lokacin da suke komawa gida daga Sokoto.
Kada ya ce, “Ban san daidai lokacin da abin ya faru ba, amma dai bayanan da jami’an tsaro suka yi mana na nuni da cewa an tare su ne a Kwanar Maharba, yayin da suke kanyar komawa gida daga Sokoto.
“Yayin da muke ta zaman jimami da zulumin jiran jiran wayar ‘yan bindigar, domin mu san dalilin yin garkuwa da su da kuma abin da suke so.”
Kamar yadda Premium Time ta ruwaito, ta ce ta samu wannan labari daga shafukan sada zumunta na WhatsApp masu yawa, waɗanda ke cike da Sakkwatawa da Zamfarawa a ciki, kuma su suka fara yaɗa labarin ɗauke da hoton basaraken.
Bawa dai a baya shi ne Hakimin Sabon Birni, kafin a maida shi Gatawa a ƙarƙashin wannan gwamnati.
Sabon Birni nan ne mahaifar Mataimakin Gwamnan Sakkwato, kuma ta na ɗaya daga cikin yankin gabashin Sakkwato da ke fama da fitintinun ‘yan bindiga tsawon shekaru da dama.
