Shugabar ƙasar Bangladesh ta arce bayan da masu zanga-zanga su ka afka fadar ta.
Faifan bidiyo da ke yawo ya nuna yadda masu zanga-zangar su ka kutsa cikin fadar suna ta ɗaukar abubuwan da suke so.
Shugabar wadda ta jima ta na mulki ance ta hau wani jirgin soja ta arce bayan da masu zanga-zanga suka ƙi bin dokar hana zirga-zirga da aka sanya a birnin Dhaka.
Shugabar an mata bore ne bayan wata doka da ta ƙirkiro wadda za ta ba da kasa 30 na ayyukan yi ga yan’uwa da kuma tsofaffin sojoji.
Aƙalla mutane 300 ne suka rasa rayukan su a dalilin wannan zanga-zangar da aka shafe kwanaki a na yi.
Jaridar the Business ta rawaito aƙalla mutane 400,000 suka fito yayin zanga-zangar wacce ta haddasa shugabar arce wa daga ƙasar.
