Kotu ta dakatar da sayar da Nigeria Air ga Ethiopian Airlines

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wata babbar kotun tarayya da ke Legas, ta haramta sayar da tashar jirgin sama ta ‘Nigeria Air’ ga ‘Ethiopian Airlines’.

Kotun ta yi hakan ne bayan da ta yi la’akari da bayanan da ke cikin ƙarar da aka shigar.

Mai Shari’a, Ambrose Lewis-Allagoa ya yi umarnin cewa, za a dakatar da shirin gwamnatin tarayya na samar da tsarin kula na kai ga Nigeria Air.

An gabatar da hukuncin ne da cibiyar masu kula gudanar da tashar jirgin da kuma wasu masana’antun jiragen sama guda biyar su ka shigar inda su ka yi nasara a ƙarar.

Mai shari’ar ya amince da duka buƙtunsu illa guda ɗaya na cewa a biya damejin Naira biliyan biyu da aka samu.

Waɗanda ke da hannu wajen shigar da ƙarar su ne; cibiyar masu kula gudanarwar tashar jirgin sama ta Nigeria Air, Azman Air Service Limited, Air peace Limited, Max Air Limited, United Nigeria Airlines Company Limited da kuma Topbrass Aviation Limited.

A gefe guda, waɗanda aka shigar da ƙarar akan su sune, Nigeria Air da Ethiopian Airlines da tsohon ministan sufuri, Hadi Sirika da Ma’aikatar sufuri ta Ƙasa da kuma tsohon Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami.

Bugu da ƙari, waɗanda suka shigar da ƙarar sun nemi kotun ta datakar da duka tsare-tsaren cinikin kamar yadda waɗanda aka shigar da ƙarar akan su suka ɓukaci a tabbatar da zaɓin su na Ethiopian Airlines.

By Babaji