Bayan gurfanar da mutane 632, Gwamnan Kano ya magantu kan masu ɗaga tutar Rasha

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

An gurfanar da mutane 632 da laifin wawure dukiyar jama’a yayin da masu zanga-zangar ke ci gaba da yin tattaki ɗauke da tutocin ƙasar Rasha a Kano,

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da gurfanar da wasu mutane 632 da ake zargi da lalata kayayyakin gwamnati da sace kayan jama’a da yayin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar,

Manhaja ta ruwaito cewa, an ga matasa masu zanga-zanga suna rera waƙoƙin nuna adawa da gwamnati da kuma riƙe da tutar kasar Rasha, a wurare irin su Mandawari da Dakata da Rimin Kebbe da Gwammja da Zoo Road da dai sauransu.

Da yake jawabi a Kano, Kakakin Gwamnan Jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake tuhuma su 632 da laifin lalata dukiyar al’umma.

Dawakin Tofa ya yi gargaɗin cewa ƙudirin gwamnatin Jihar Kano na wanzar da zaman lafiya ba abu ne da gwamnati zata yi wasa da shi ba, inda ya ƙara da cewa waɗanda aka samu da laifin ɓarna za su fuskanci doka.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin jihar na shirin samar da ɗimbin shirye-shiryen horas da matasa sana’o’i daban-daban domin inganta rayuwar su, domin daƙile yiyuwar amfani da su wajen karya doka da oda.

Kakakin ya kuma sanar da cewa za a kafa kwamitin bincike na musamman da zai binciki waɗanda ke da hannu wajen kashe-kashe da sace-sacen kayan jama’a a jihar.

Kwamitin zai tantance musabbabin kashe-kashe da lalata gine-ginen gwamnati, in ji shi.

Ya ƙara da cewa masu zanga-zangar da suke ɗauke da tutocin ƙasar Rasha ba su da alaƙa da gwamnati, don haka ya buƙaci hukumomin tsaro da su bankaɗo waɗanda ke ingiza su da kuma manufarsu.

Kazalika, ya bayyana cewa masu zanga-zangar na gaskiya a jihar sun miƙa kokensu da buƙatunsu ga gwamnati, wanda ya ce za a miƙa su ga shugaba Bola Tinubu.

By ukarofi