Matasa a garin Jos sun ƙarya dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya, inda da daman su suka fito yin zanga-zangar.
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda jami’an tsaro, sojoji da ƴan sanda su kayi ƙokarin shawo kan matasan amma abun ya ci tura, sai dai rabuwa su ka yi da su.
In ba mu manta ba, Gwamnan Jihar Jos, a safiyar yai ya sanya dokar hana zirga-zirga a wasu sassa na cikin Jihar saboda gudun tashin hankali ganin yadda zanga-zangar ta fara rikiɗewa saboda shiga ɓatagari.
